An Shiga Rana Ta Farko Na Taron Bayar Da Horo Ga Matasa Akan Yadda Zasu Samu Kudi Ta Wayar Hannu Wanda Cibiyar KVC Katsina Ta Shirya.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08092025_201544_FB_IMG_1757362491683.jpg


‎Daga Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times.
‎Daddadiyar cibiyar bayar da horo ga matasa akan yadda zasu koyi sana'o'in hannu mai suna (Katsina Vocational Training Center, Katsina), wadda ta kwashe tsawon shekaru fiye da ashirin tana horas da matasa akan yadda zasu tsayu da kansu ta hanyar sana'o'in hannu, wadda marigayi MD Yusuf ya assasa.
‎A ranar Litinin 08 ga watan Satumba, na shekarar 2025, cibiyar wadda take da reshe a jihar Katsina, a unguwar Kerau, ta yi hadin gwiwa da Paracha Family Abuja, domin kara samar da cigaba ga matasa, da ma al'umma baki daya. Sun shirya taron horas da matasa na tsawon kwanaki uku akan yadda zasu koyi sana'o'i da kuma samun kuɗi ta wayoyin hannu su.
‎An yi ma taron take da "AMFANI DA WAYAR HANNU WAJEN SANA'O'I DA NEMAN KUDI" wanda aka fara a yau Litinin za a gama a ranar Laraba ta wannan watan da muke ciki na Satumba, a dakin taro na sakatariyar gwamnatin jihar Katsina. 
‎A rana ta farko an fara horas da mahalarta taron akan wasu muhimman abubuwa wadanda suke kunshe cikin wayoyin hannu, wadanda ke taimaka ma mutum wajen adana bayanan sirri, hanyoyin bi di-di-ki, da kuma hanyar da zaka gano inda kake ko inda zaka, wanda a turance ake kiranta da (Map).
‎Bugu da kari an zurfafa ma mahalarta taron akan yadda zasu kula da kafofin su na sada zumunta, da kuma yadda zasu kiyaye daga barayin satar bayanai ko satar asusu (Harkers). Sannan kuma an yi duba tare da nuna masu yadda zasu yi amfani da wasu boyayyun na'urori wajen gane yanayi (Weather) da kuma na'urar da zasu ajiye bayyana lafiyar su domin neman agajin gaggawa a lokacin da wata matsala ta same su.

Follow Us