"Mutane su kare kawukansu daga 'Yan bindiga" Malam Musa Ibrahim Faskari, a Khudbar Juma'a
- Katsina City News
- 22 Sep, 2023
- 907
Fitaccen malamin addinin Muslunci a jihar Katsina, Sheikh Musa Ibrahim Faskari ya shawarci mutane su kare kansu daga hare-haren yan bindiga.
Faskari ya ba da shawarar ce ga yankunan da ke fama da hare-haren 'yan bindiga da su dauki makamai don kare kansu.
Malamin ya bayyana haka ne yayin gabatar da hudubar sallar Juma'a, a wani fai-fain bidiyo da aka yada a kafafen sadarwa.
Ya ce addinin Musulunci ya karfafi mabiya addinin da su dauki makamai don kare kansu idan ana kai musu hare-hare.
Ya ce addinin Musulunci ya bai wa Musulmai damar kare kansu daga addininsu da lafiya da dukiya da iyalai da kuma martabarsu.
"Mu na ganin yadda jami'an tsaro ke cike a yankunan mu amma kuma mu na fama da hare-haren 'yan bindiga.
"'Yan uwanmu sun zama bayin wasu a garuruwansu, su na aikin gona a banza, ba za mu yadda da cin zarafi ba.
"Dukkanmu ba ma son mutuwa kuma ba ma kokarin hada kai don kawo karshen abin."
Jihohin Arewa maso Yamma na fama da hare-haren 'yan bindiga a yankuna da dama