An samu saukin kai hare-hare a wasu yankunan Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06092025_081024_IMG-20250906-WA0039.jpg


...Al'ummomi ke sasanci da ‘yan bindiga ko gwamnati?

Daga Muhammad Kabir Katsina

Wani bincike da DCL Hausa ta gudanar a wasu bangarorin da aka ƙulla sasanci da 'yan fashin daji a jihar Katsina, ta gano yadda aka samu saukin kai hare-haren ‘yan bindiga a yankunan.

A wani faifan bidiyo da ya nuna yadda wakilan DCL Hausa suka yi tattaki har garin Malam Ali da ke a karamar hukumar Jibia, inda kasurgumin shugaban 'yan bindiga, Lanƙai yake zaune da yaransa dauke da muggan makamai.

Lanƙai, wanda ya yi kaurin suna a yankin karamar hukumar Jibia, ya zama shugaban yan bindigar da ke jagorantar yaransa wajen addabar al'ummomin yankin.

Ko sasanci da 'yan bindigar ya haifar da ɗa mai ido a yankin?

DCL Hausa ta tattaro wasu bayanai da ke nuna cewa, kimanin watanni takwas da yin sasanci, ba a kara samun wani hari ba a yankin.

Sai dai barayin dajin sukan ratsa ta kauyukan da aka yi sulhu su wuce ba tare da sun taɓa kuwa ba, suje wasu kauyukan makwabta su kai farmaki.

DCL Hausa sun gano al'ummomin yankin sun koma hada-hadarsu ta bangarori da dama da suka hada da noma,kiwo da kasuwanci. 

Barayin, sukan shigo har cikin gari su yi hada-hadar su ba tare da an taba su ba, haka ma al'ummomin garin Jibia sukan shiga daji ba tare da wata fargaba ba.

Wata majiya ta ce 'yan bindigar su ne da kansu suka nemi a yi sasanci da mutanen gari domin a zauna lafiya.

Ya zuwa yanzu dai kananan hukumomi biyar ne suka rungumi sasanci a jihar.

A baya dai, gwamnatin Malam Dikko Umar Radda ya sha alwashin ba zai yi sulhu da yan bindiga ba, amma, a cewar sa idan ‘yan fashin daji suka kawo kansu, suka nemi a yi sulhu, za a yi.

Follow Us