An Kaddamar da Taron Malaman Laburari na Ƙasa karo na 9 a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes01092025_194056_FB_IMG_1756755478162.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times | 1 ga Satumba, 2025

An kaddamar da taron shekara–shekara na Malaman Laburare na Ƙasa karo na 9 a dandalin taro na Sakatariyar Jihar Katsina a ranar Litinin, inda mahalarta suka nuna damuwa kan yadda ake barin ɗakunan karatu a sassan ƙasar cikin mawuyacin hali.

Taron, wanda yake gudana daga 1 zuwa 2 ga Satumba, na gudana ne ƙarƙashin taken “Sabunta Ɗakunan Karatu na Jama’a: Kirkire-kirkire, Haɗa Kan Jama’a da Ƙarfafa Gwiwa.”

A jawabinta, Babbar Daraktar Ɗakin Karatu ta Ƙasa, Farfesa Chinwe Veronica Anunobi, ta yaba wa Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, bisa matakan da gwamnatinsa ta ɗauka wajen farfaɗo da ɗakunan karatu a jihar, wadanda a cewarta sun kusa rushewa kafin zuwansa mulki.

Sai dai ta nuna damuwa da cewa yawancin ɗakunan karatu na jihohi a Najeriya sun shafe sama da shekaru 25 ba tare da an ɗauki kwararru ko sabunta littattafansu ba, wasu ma an rufe su ko aka mayar da wuraren a wasu ayyuka.

“Wannan babban kalubale ne ga ƙasa wadda sama da mutane miliyan 20 ba su iya karatu da rubutu ba,” in ji ta. “Idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, hangen nesa na waɗanda suka assasa ɗakunan karatu na jama’a zai rushe.”

Farfesa Anunobi ta jaddada cewa lokaci ya yi da ɗakunan karatu a Najeriya za su zamo cibiyoyin koyon fasahar zamani, adana al’adu da kuma wuraren haɗin gwiwar al’umma. Ta ce duk wani sabon tsari ya kamata ya kasance kyauta, mai aminci, kuma kowa na da damar amfani da shi.

Ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da kwamitocin kula da ɗakunan karatu su aiwatar da shawarwarin taron, tana mai cewa haɗin kai shi ne hanyar da za ta taimaka wajen mayar da ɗakunan karatu cibiyar ilimi, cigaba da ɗorewar tattalin arziki.

A nasa jawabin da Kwamishinan Ilimin Fasaha, Sana’o’i da Manyan Makarantu na Katsina, Alhaji Isah Muhammad Musa, ya gabatar a madadin Gwamna Dikko Radda, ya bayyana cewa duk da tasirin fasahar zamani da wayoyin hannu wajen neman ilimi, akwai buƙatar a ci gaba da raya ɗakunan karatu domin su kasance cibiyoyin bincike da kirkire-kirkire.

Ya yaba wa ƙungiyar masu kula da ɗakunan karatu bisa jajircewar ta wajen inganta harkar karatu, tare da buƙatar ƙarin zuba jari wajen horas da ma’aikata.

Kwamishinan ya ce gwamnatin Katsina ta ɗauki ilimi a matsayin ginshiƙin manufofinta, inda aka zuba jari a makarantun sakandare da na gaba da sakandare, da kuma kafa makarantu na musamman guda uku domin shirya matasa cikin ilimin zamani na fasahar intanet.

Ya kara da cewa, “Gwamnati na ganin babu ci gaban ilimi idan babu tsaro, saboda haka tana ci gaba da tallafa wa tsare-tsaren tsaro don tabbatar da cewa makarantunmu da al’ummarmu sun kasance cikin yanayi mai kyau da ya dace da karatu.”

Ya kuma yaba wa Hukumar Laburare ta Ƙasa bisa kawo wannan babban taro Katsina, yana mai fatan sakamakon tattaunawar zai taimaka wajen gyara da farfaɗo da ɗakunan karatu a fadin Najeriya.

Follow Us