Dangote Ya Kulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 2.5 da Habasha Don Gina Masana’antar Takin Zamani

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28082025_135329_Screenshot_20250828-143444.jpg

Katsina Times

Attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya sanya hannu kan yarjejeniyar dala biliyan 2.5 da gwamnatin Habasha domin gina babbar masana’antar takin zamani a ƙasar, a matsayin wani muhimmin mataki na rage shigo da taki daga ƙetare da kuma ƙarfafa samar da abinci a nahiyar.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a Addis Ababa tsakanin Dangote Group da Ethiopian Investment Holdings (EIH), inda Dangote zai mallaki kaso 60% na hannun jari, yayin da gwamnatin Habasha ta rike ragowar kaso 40%.

Masana’antar za a gina ta ne a yankin Somali na Habasha, inda ake sa ran za ta samar da ton miliyan uku na urea a duk shekara. Wannan shi ne karo na farko da Dangote zai kafa masana’antar taki a wajen Najeriya, abin da ke nuna ƙaruwar shirin fadada jarinsa a nahiyar.

Habasha na kashe fiye da dala biliyan ɗaya duk shekara wajen shigo da taki daga waje domin tallafawa noma, wanda sama da kashi 70 cikin 100 na al’ummar ƙasar ke dogara da shi. Masana’antar da za a gina za ta samu haɗin kai da filayen iskar gas ta hanyar bututun musamman, kuma tana iya rage yawan shigo da taki har ma ta ba ƙasar damar fitar da taki zuwa wasu ƙasashe a nan gaba.

An tsara ginin ya kai tsawon watanni 40 kafin kammalawa. Wannan aiki haɗin gwiwa ne tsakanin Dangote Group da EIH, wanda ke kula da kadarorin gwamnati don bunƙasa tattalin arziƙi. Daga baya ana iya ƙara samar da sauran takin zamani irin su ammonium nitrate da ammonium sulfate.

Ga Habasha, wannan masana’antar za ta ƙarfafa tsaron abinci tare da rage kashe kuɗaɗen waje wajen shigo da taki. Ga Dangote kuma, wanda rahotannin Bloomberg suka kiyasta dukiyarsa a dala biliyan 28.7, wannan wani babban mataki ne wajen cike gibin bukatar taki a Afirka.

Bayan sauka daga mukaminsa na shugaban Dangote Cement Plc, Dangote ya karkata ga masana’antar taki da tace mai, domin cimma burinsa na rage dogaro da shigo da kayayyaki daga ƙetare da kuma ƙara ƙarfin noma a nahiyar.

Wannan ya fito fili a shirin Habasha, inda ake sa ran Dangote Fertilizer Limited za ta shiga kasuwar hannun jari a Najeriya (NGX) da darajar fiye da dala biliyan 3. A Najeriya, masana’antar da ke Ibeju-Lekki, Lagos—wacce ita ce mafi girma a nahiyar—na da ƙarfin samar da ton miliyan 3 na urea a shekara, fiye da bukatar manoman ƙasar sau biyu.

Ana sa ran wannan zai rage farashin taki ga manoma a Najeriya tare da ciyar da sauran kasuwannin yankin gaba. Bloomberg ya kiyasta darajar masana’antar a dala biliyan 3.02 ko da tana aiki da rabin ƙarfin ta, abin da ke nuna irin dimbin damar da ke akwai a nan gaba.

Follow Us