Jam'iyyar APC mai mulkin jihar Katsina, ta bayyana tsaro a matsayin abin da ya fi komai muhimmanci har da siyasa a halin da ake ciki yanzu a jihar.
Mataimakin shugaban jam'iyyar, Alhaji Bala Abu Musawa ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya kira 'yanjarida ciki har da jaridun Katsina Times a ranar Larabar nan.
Bala Musawa ya bayyana cewar a halin yanzu, damuwar Jam'iyyar ta APC a jihar ita ce Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya samu nasara kan matsalar tsaro da ta addabi jihar.
"Shi ya fi damunmu fiye da siyasar. Amma siyasa muna nan mun tara, za mu fadi idan lokaci ya zo," in ji Musawa.
Ya nanata cewa duk da wannan kalubale na tsaro, hakan bai hana hannayen gwamnatin jihar sun kai ga al'umma ba, inda ayyukan raya kasa suka shiga dukkan mazabu 361 na jihar.
"Babu mazaba guda daya da za a ce ayyukan Malam Dikko Umaru Radda ba su kai ba," ya tabbatar.
Batun Hutun Lafiya Na Gwamna Radda.
A game da tafiyar hutun neman lafiya da gwamnan jihar ya yi bayan hatsarin mota da ya samu, Musawa ya yi watsi da maganganun da 'yan'adawa suka yada, yana mai cewa, "Ai ko kai magidanci mai iyali kadan kana jin nauyin shugabanci, balle gwamna mai shugabantar jiha. Dole ne ya je hutun neman lafiya don ya dawo ya ci gaba da shugabanci da kyau."
Ya yaba wa Mukaddashin Gwamnan jihar, Honorabul Faruk Lawal Jobe, bisa kwarewarsa wajen tafiyar da gwamnati a wannan lokaci. Musawa, ya ce shi dai a tarihin saninsa da siyasa bai taba ganin gwamna ya bar rikon gwamnati hannun mataimakinsa ba sai ga Malam Dikko Radda, ban da lokacin marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua da ya ba wa Tukur Jikamshi rikon gwamnati.
Martani Ga Masu Adawa.
Musawa ya bayyana jam'iyyar ADC a matsayin jam'iyyar masu jin haushin rasa mulki, wanda hakan ke jawo masu surutu da zarge-zarge.
"Wasu daga cikinsu sun samu dama a baya amma suka kasa tsinana komai, yanzu kuma suna caccakar gwamnati saboda ba su da mulki," in ji shi.
Ya ce sakamakon zabukan cike gurbi da aka yi a makon da ya gabata ya nuna karfin jam'iyyar APC, wanda kusan za a ce ya kada gamayyar 'yan'adawa baki daya.
Martani Kan Batun Kudin Tsaro.
Game da zargin kashe makudan kudade a fannin tsaro ba tare da nasara ba, Musawa ya ce:
"Ban yi tsammani wanda aka ba shi damar shugabantar tsaro na tsawon shekara takwas zai zo ya ce makudan kudaden da aka kashe ba su da amfani. Illar da 'yanbindiga suka haifar ta ninka kudin da ake kashewa, domin rai, dukiya da lafiyar talakawa da ake karewa."
Fatan Alheri Ga Katsina.
Daga karshe, Musawa ya yi wa al'ummar Katsina albishir da karin ci gaba tare da ganin sabbin ayyukan raya kasa bayan dawowar gwamnan daga hutun neman lafiya. Ya roki jama'a da su ci gaba da yi wa gwamnati addu'a domin samun nasarar shawo kan matsalar tsaro da ake kan ganin hasken nasarar haka a 'yankwankin nan.