Yan Majalisar Tarayya da Sanata Dandutse Sun Ziyarci Al'ummar Mantau Don Ta’aziyyar Harin ’Yan Bindiga, Sun Kuma Yi Alkawarin Ƙarin Tsaro

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24082025_225209_FB_IMG_1756075700514.jpg



Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times | 24 ga Agusta, 2025

Wata babbar tawaga ta manyan ’yan majalisar tarayya, shugabannin gargajiya da na siyasa daga Shiyyar Funtua, karkashin jagorancin Sanata Muntari Dandutse, shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar dattawa, sun kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummar Kauyen Mantau da ke gundumar Karfi a Karamar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina, a ranar Lahadi.

Ziyarar ta biyo bayan mummunan harin da ’yan bindiga suka kai makon da ya gabata a kauyen, inda aka kashe akalla mutane 28 tare da yin garkuwa da sama da mutum 80. Duk da cewa daga baya an saki mafi yawan wadanda aka sace, harin ya bar jama’a cikin tashin hankali da bakin ciki.

Tawagar ta kunshi ’yan majalisar wakilai daga dukkan kananan hukumomin 11 na Shiyyar Funtua, shugabannin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da sauran fitattun mutane. Wannan ziyara ta kasance don jajanta wa iyalan da abin ya shafa da kuma nuna cewa gwamnati ba za ta bar su su fuskanci kalubale su kaɗai ba.

Da yake jawabi, Sanata Dandutse ya bayyana alhini mai zurfi, yana mai cewa wannan fitina ce mai girma wadda ta bukaci juriya da addu’a. Ya yi Allah-wadai da kashe-kashe, sace-sace da barna da ’yan ta’adda ke haddasawa a Katsina, inda ya ce majalisar dattawa za ta dauki matakan gaggawa wajen dawo da zaman lafiya.

“Babu wani shugaba da zai so ya ga jama’arsa suna rayuwa cikin tsoro da tashin hankali. Mun riga mun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar da ƙarin jami’an tsaro a Malumfashi da kewaye. Akwai shirin kafa hedkwatar rundunar sojoji tsakanin Karfi da Malumfashi, tare da kafa sansanin Mobile Police, kowannensu na ɗauke da akalla jami’ai 600. Bugu da kari, za a tallafawa ’yan sa-kai domin su kara kaimi wajen tunkarar ’yan bindigar,” in ji shi.

Ya kara da cewa wannan yaki na bukatar sadaukarwa da jarumtaka: “Na yi rantsuwa, ko da za mu rasa rayukanmu, za mu tsaya tsayin-daka domin ganin an samu adalci. Babu wata gwamnati da za ta zauna ta kalle ka, ana kashe mutane, ana fyade da kona gida, ba tare da ɗaukar mataki ba.”

A wani bangare na taimakon gaggawa, Sanata Dandutse ya sanar da bada kayan agaji da suka kai kimanin naira miliyan 10, ciki har da buhunan shinkafa 100, masara 100 da kuma buhunan siminti 200 domin sake gina masallacin da aka lalata a lokacin harin. Ya ce wannan mataki ne na rage radadin al’umma da kuma karfafa gwiwarsu.

Cikin tawagar sun hada da shugaban Karamar Hukumar Malumfashi, ’yan majalisar tarayya na Malumfashi/Kafur da Musawa/Matazu, mataimakin shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta jihar Katsina (ALGON) Rabo Tambaya Danja, Mai Shari’a Sadiq Abdullahi Mahuta, da Mai garin Karfi, tare da sauran dattijai da shugabannin al’umma.

Shugabannin yankin sun nuna godiya bisa wannan ziyara, suna mai cewa hakan alama ce ta nuna kulawa. Duk da haka, sun jaddada bukatar gwamnati ta hanzarta tura jami’an tsaro domin kauyukan karkara su sami kariya daga hare-haren da suka addabi manoma da iyalai.

A makon da ya gabata, kauyen Mantau ya shiga cikin makoki bayan da ’yan bindiga suka farmaki al’ummar garin da daddare, inda suka kashe sama da mutane 28 tare da yin garkuwa da wasu da dama. Masu garkuwar sun kuma lalata gidaje da kadarori. Duk da cewa daga baya an saki wasu daga cikin wadanda aka dauke, jama’a sun ce har yanzu akwai tsananin tsoro da fargabar sake aukuwar hari.

Sanata Dandutse ya kammala jawabin nasa da addu’a mai zafi ga wadanda ke da hannu a aikata wannan mummunan laifi: “Za mu ci gaba da rokon Allah, domin ba su fi karfinSa ba. Allah Ka tona asirin duk wanda ke da hannu a wannan ta’asa, Ka kuma hallaka shi.”

Masu sharhi na ganin wannan ziyara ta ’yan majalisar da shugabannin siyasa na iya kara jan hankalin gwamnatin tarayya kan lamarin tsaro, musamman ganin yadda matsalar ta’addanci ta ci gaba da barazana ga rayuka, amincin jama’a da harkar noma a jihar Katsina.

Follow Us