Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 23 ga Agusta, 2025
Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa tana ci gaba da ɗaukar matakan ƙarfafa yaki da ’yan bindiga, tare da kaddamar da sabbin kayan aikin tsaro da kuma ceto mutane 72 da aka yi garkuwa da su.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Dr. Nasiru Mu’azu Danmusa, ya sanar da haka a yau Asabar yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Ofishin Mataimakin Gwamna, Gidan Gwamnati a Birni Katsina.
Dr. Danmusa ya yi ta’aziyya ga al’ummomin da aka kai wa hare-hare a makon da ya gabata musamman na Malumfashi, a Gidaman Mantau, inda aka rasa rayuka 28.
“A madadin gwamnati, muna mika sakon ta’aziyya ga iyalai da al’ummomin da abin ya shafa. Haka kuma muna gode wa Allah bisa nasarar ceto mutane 72 da aka yi garkuwa da su, bayan haɗaɗɗen aikin jami’an tsaro,” in ji shi.
Ya bayyana cewa matsalar ta’addanci da satar mutane na buƙatar haɗa dabaru na soji da na al’umma. A cewarsa, Gwamna Dikko Umar Radda ya riga ya nuna ƙarfin gwiwa ta hanyar zuba sama da Naira biliyan 36 wajen inganta harkokin tsaro a jihar.
Kwamishinan ya ce yanzu haka Katsina tana daga cikin jihohin Arewa da suka fi kowace yawan kayan aikin tsaro, in Banda jihar Borno. Ya ƙara da cewa kwanan nan Gwamna ya sayo sabbin motoci masu sulke guda takwas, wanda ya kai jimillar motocin da jihar ke da su zuwa 43, kuma an riga an baza su a muhimman wuraren da ake fama da hare-hare.
Ya bayyana cewa jami’an tsaro sun bazu a kananan hukumomi da dama da ke fama da hare-haren ’yan bindiga.
Yayin da yake yabawa jami’an tsaro bisa namijin ƙoƙarinsu, Dr. Danmusa ya jaddada muhimmancin shiga al’umma wajen yaki da ta’addanci:
“Wannan matsala daga tushe take fitowa, kuma dole a samo mafita daga tushe. Tsaro ba aikin gwamnati kaɗai ba ne, aikin kowa ne a cikin al’umma.”
Ya yi gargaɗi ga masu ƙoƙarin siyasantar da batun tsaro musamman a lokacin damina, lokacin da manoma ke shiga cikin ƙauyuka.
“Wannan ba lokaci ba ne na yin siyasa da batun tsaro. Idan kana ƙaunar jihar Katsina, ka bayar da gudummawa. Ƙofofinmu a buɗe suke ga kowa don bayyana yadda ake kashe kuɗaɗen tsaro. Gwamnati tana da alhakin bayani ga jama’a.”
Kwamishinan ya kammala da kira ga jama’a da su kasance masu haɗin kai, addu’o’i da kuma bayar da goyon baya ga jami’an tsaro domin tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar Katsina.