Katsina Times
Majiyoyi daban daban a garin Yar goje dake karamar hukumar kankara jahar katsina sun tabbatar da ganin mugun dan ta addar nan da ya jagoranci mummunan harin garin gidan mantau, wanda aka kashe mutane masu yawa aka tafi da wasu cikin daji mai suna Mustapha Babaro.
Mutanen garin sun tabbatar wa da jaridun Katsina Times cewa Mustapha Babaro yazo garin ne domin duba gonar sa da kuma shanunsa dake kiwo a garin.
Mutanen sun tabbatar wa da Katsina Times cewa Babaro ya zo garin daga shi sai masu tsaron shi guda da misalin karfe uku na yammacin yau juma'a. 22, ga wata
Babaro yayi kamar awa biyu zaune kasan wata bishiya 'yan garin na zuwa suna kai masa gaisuwa.
Garin 'yar goje sun yi sasanci da Babaro don haka suna bashi duk wani hadin kai da goyon baya.
Katsina times
Www.katsinatimes.com
Facebook Page. ; Katsina City News
Jarida Taskar labarai
07043777779