Gwamnatin Tarayya Za Ta Samar da Ƙaramar Tashar Lantarki ga Makarantun Gaba da Sakandare Nan da 2026

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan da shekarar 2026, dukkan makarantun gaba da sakandare a ƙasar za....

Katsina City News August 21, 2025  ·  12:00 AM
| 975 Views
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan da shekarar 2026, dukkan makarantun gaba da sakandare a ƙasar za su samu Ƙaramar Tashar Lantarki domin samar da isasshen wutar lantarki. Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana haka a wajen ƙaddamar da sabon ɗakin taro na Olatunji Bello Auditorium da aka gina a Jami’ar Jihar Legas (LASU). Ya ce wannan wani alƙawari ne na Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga ɗalibai da jami’o’i a faɗin ƙasa.

Alausa ya bayyana cewa an amince da ƙaramar tasahar lantarkin mai ƙarfin Megawatt 5 domin harabar Epe dake LASU, yayin da TETFund za ta samar da Megawatt 11 domin babbar harabar jami’ar da ke Ojo. Ya ce samun isasshen wutar lantarki zai ba matasa damar ƙara bincike, ƙirƙira da fasaha, wanda zai taimaka wajen bunƙasa ci gaban ƙasa.

Advertisement

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 7 + 7?