Zaharaddeen Ishaq Abubakar | KatsinaTimes
Karamar hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina na ci gaba da fama da matsalar tsaro, yayin da hare-haren ’yan bindiga ke ƙara ta’azzara a yankunan karkara. Duk da ikirarin gwamnati na ƙara shawo kan lamarin, jama’a na cewa rayuwarsu na cikin tsananin fargaba da rashin tabbas.
Hare-Hare Uku a Mako Ɗaya
A cikin makon da ya gabata, an samu rahotannin hare-hare a ƙauyuka uku na arewacin Malumfashi.
A ranar Litinin, ’yan bindiga sun kai farmaki Gidan Maijimina inda suka kashe mutum ɗaya. A wani hari dabam, sun kashe mutane biyu tare da yin awon gaba da shanu. Ranar Alhamis kuma, a Gidan Barau, sun kashe wani mutum daga Gidan Dan Ango, sannan suka kwashe shanu da wayoyin hannu. A ranar Lahadi kuwa, sun shiga Gidan Hazo, suka fasa shagon wani mai kasuwanci, suka kwashe kayan abinci da lemo, sannan suka harbi mutane biyu da ke jinya yanzu haka a Asibitin Katsina.
Mazauna Sun Koka
“Mun rasa kwanciyar hankali gaba ɗaya. Duk dare muna bacci cikin fargaba. Muna roƙon gwamnati ta kawo mana ɗauki kafin al’amura su ƙara muni,” in ji wani mazaunin Gidan Hazo.
Haka kuma wani manomi daga Gidan Barau ya ce: “Rayuwar manoma ta tsaya cik. Ba mu iya zuwa gona cikin kwanciyar hankali. Idan haka ta ci gaba, tattalin arziƙin ƙauyukanmu zai durƙushe.”
Masana tsaro sun bayyana cewa satar dabbobi da kayan abinci na nuna cewa ’yan bindiga suna sauya salo saboda tsananin matsin tattalin arziƙi a dazuka.
Duk da ikirarin gwamnatin Jihar Katsina cewa tana aiki tare da jami’an tsaro da ƙananan hukumomi don shawo kan matsalar, jama’a na cewa ba su ganin tasirin hakan a aikace.
Wani jami’in tsaro da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce: “Akwai ƙarancin kayan aiki da bayanan sirri wajen magance hare-haren. Sai an ƙara samar da kayan aiki da ingantaccen sa ido kafin a samu sauyi.”
Binciken Katsina Times ya gano cewa wasu ƙauyuka kamar Koro, Gidan Dandaudu, Unguwar Gishiri, Gidan Maijimina, Gidan Lado da Zarangozai sun shiga yarjejeniya da ’yan bindiga, inda aka tilasta musu biyan diyya da ta kai naira miliyan 15.
Sai dai al’umma na ganin hakan tamkar ƙara wa ’yan ta’adda ƙarfin gwiwa ne. “Biyan kuɗi ga ’yan bindiga na ƙara musu damar cin karen su ba babbaka. Muna kira ga gwamnati ta kawo mana mafita,” in ji wani dattijo.
Masana sun yi gargadin cewa yawan gudun hijira da barin ƙauyuka zuwa birane na iya jefa tattalin arziƙin jihar cikin matsala, musamman a bangaren noma.
A halin yanzu dai, Malumfashi da sauran kananan hukumomi na jiran matakan gaggawa don dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.