Fadar shugaban ƙasa ta yaba da ƙwazon Ribadu a matsayin NSA a watanni 25 da fara aiki

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes18082025_180200_Nuhu-Ribadu-NSA.jpg

 Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa watanni 25 da Malam Nuhu Ribadu ya kwashe a matsayin Mai baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA) sun zama juyin juya hali a yaki da ta’addanci, ’yan fashi da makami da sauran barazanar tsaro.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, ya ce nadin Ribadu ya samar da sakamako a fili, ciki har da cafke manyan masu hannu a hare-haren ta’addanci, rage yawaitar hare-haren ’yan fashi a Arewa maso Yamma, ƙaruwar man fetur da ake samarwa ƙasa da miliyan ɗaya zuwa kusan miliyan 1.8 a kowace rana, da kuma rage rikicin ƙabilanci a wasu jihohi.

Haka kuma, ya ce Ribadu ya taka muhimmiyar rawa wajen raunana kungiyar IPOB/ESN, tare da dawo da tsaro a manyan hanyoyi kamar Abuja-Kaduna.

Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa nasarorin sun samu ne da goyon bayan Shugaba Tinubu wanda ya inganta walwalar sojoji, ya ƙara sayen sabbin kayan aiki da kuma amfani da fasaha a harkokin leƙen asiri da sa ido.

Duk da haka, ta ce akwai sauran ƙalubale, amma tsarin tsaro ya fi ƙarfi a yanzu, inda manoma ke fara komawa rayuwa ta yau da kullum.
Daily Nigerian 

Follow Us