Yar’adua Ya Gana da Magoya Baya, Ya Nemi Goyon Bayan Tafiya a Jam’iyyar ADC A Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes16082025_203709_FB_IMG_1755376496945.jpg



Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina, 16 ga Agusta 2025

Sanata Abubakar Sadiq Yar’adua, tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen 2023, ya gana da magoya bayansa daga yankin Katsina ta tsakiya domin neman goyon baya ga sabuwar tafiyarsa a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Taron, wanda aka gudanar a ranar Asabar a gidan Yar’adua da ke unguwar GRA cikin birnin Katsina, ya haɗa da wakilai daga kananan hukumomi 11 da suka haɗa da Katsina, Kaita, Dutsinma, Kurfi, Batagarawa, Charanci, Jibia, Danmusa, Rimi da sauran su.

Yar’adua, wanda ya taba kasancewa ɗan majalisar wakilai ta tarayya da kuma sanata mai wakiltar Katsina ta tsakiya, ya sauya sheka zuwa ADC a makon da ya gabata, inda yanzu yake rike da mukamin Babban Sakataren Tuntuɓa na ƙasa

A jawabin sa, Yar’adua ya bayyana dalilin ficewarsa daga APC, yana mai cewa manufar ADC ta fi dacewa da burinsa na ganin adalci, gaskiya da haɗin kai a siyasa. Ya bukaci magoya bayansa da su rungumi tafiyar cikin natsuwa da fahimta ba tare da tilastawa kowa ba.

“Wannan tafiya ce ta gaskiya da amana. Ba mu zo nan domin tilastawa kowa ba, sai dai domin mu jawo hankalin jama’a cikin gaskiya da adalci,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa ADC a Katsina za ta fara shirin kaddamar da rijistar mambobi tare da rarraba katin zama cikakken ɗan jam’iyya, inda ya ce yana tattaunawa da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar Katsina guda bakwai da ke shirin shiga jam'iyyar hada ka ta ADC.


Duk da haka, Yar’adua ya ja hankalin magoya bayansa cewa siyasa cike take da ƙalubale, don haka akwai bukatar juriya da hakuri. “Muna da tsari a matakin ƙasa wanda zai tabbatar da adalci ga kowa da kowa,” ya ƙara da cewa.

Taron ya samu halartar manyan tsoffin jami’an gwamnati, daraktoci da masu ruwa da tsaki a siyasar jihar. Daga cikinsu har da tsohon mai taimaka wa gwamnan Katsina na musamman kan harkokin lafiya, Hon. Jabiru Yusuf Yau-Yau daga ƙaramar hukumar Batsari, wanda ya bayyana cikakken goyon bayansa ga tafiyar ADC.

Shigar Yar’adua cikin jam’iyyar ADC na kara ɗaukar hankali a siyasar Katsina, abin da masana ke ganin zai iya taka muhimmiyar rawa wajen tsara makomar zaɓen 2027 a jihar.

Follow Us