JESSICA DA DOLPHIN: Labarin Ƙirƙirar AI Mai Sosa Zuciya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12082025_203350_FB_IMG_1755030737447.jpg

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar 

Rahoton da ya bazu a shafukan sada zumunta da ke cewa wata mai horas da kifayen ruwa ‘yar Amurka mai suna Jessica Radcliffe ta mutu sakamakon harin wani kifi dolphin ko orca yayin da take gudanar da wasa da shi, an tabbatar da cewa karya ce gaba ɗaya.

Labarin, wanda ya fara yaduwa a TikTok da wasu kafafen sada zumunta a ƙarshen watan Yuli 2025, ya yi ikirarin cewa “Jessica Radcliffe mai shekaru 23” ta mutu yayin wani shirin nune-nune a wurin boge mai suna "Pacific Blue Marine Park". A Wata sigar labarin sun yi zargin cewa kifin ya fusata ne saboda jinin al’ada ya shiga cikin ruwan.

Sai dai bincike mai karfi da jaridun ƙasa da ƙasa suka gudanar ciki har da The Economic Times, Hindustan Times, E! Online da The Sun ya nuna babu wata mace mai wannan suna a duk wata cibiyar horas da kifayen ruwa a Amurka ko a ƙasashen waje. Babu wani rajista a hukumomin gwamnati ko a kafafen yada labara da ya tabbatar da wanzuwar ta.

“Wannan misali ne na zahirin karya da aka kirkira ta hanyar fasahar AI,” in ji rahoton E! Online, inda ya bayyana cewa bidiyon da ake yadawa ya nuna alamun hadin kwamfuta kamar motsin ruwa marar daidaito, haske da ke bambanta da hoton, da kuma matsalar daidaituwar fuska.

Binciken Hindustan Times da Katsina Times ta gani na 7 ga Agusta, 2025, ya tabbatar cewa sunan Jessica da wurin "Pacific Blue Marine Park" duk kirkira ne, inda hoton da bidiyon da aka yada an gina su ne ta amfani da fasahar kirkirar hotuna ta kwamfuta (generative AI).

Ko da yake labarin Jessica Radcliffe karya ne, amma an taɓa samun faruwar hare-haren orca a zahiri. A 2010, wata ƙwararriyar mai horas da kifayen ruwa a SeaWorld Orlando mai suna Dawn Brancheau ta mutu bayan kifin orca mai suna Tilikum ya ja ta zuwa cikin ruwa, kamar yadda Orlando Sentinel ta ruwaito. A shekarar 2009 kuma, Alexis Martínez ya mutu a Loro Parque, Tenerife (Spain) bayan kifin Keto ya buge shi, kamar yadda BBC News ta tabbatar.

Masana sun yi gargadin cewa irin waɗannan labaran karya na AI suna yaduwa cikin sauri saboda yadda suke ƙunshe da hotuna masu kama da na gaske da labarin da ke tayar da hankali.

“Haɗin hoto mai kama da na zahiri da labari mai tada hankali yana sa irin wannan karya ta yi saurin yaduwa, amma hakan na rage amincewar jama’a ga sahihan labarai,” in ji masanin nazarin kafofin yada labarai, Priya Nair, ga The Economic Times.

Lamarin Jessica Radcliffe ya zama babban misali na yadda ake buƙatar masu amfani da shafukan sada zumunta su tabbatar da sahihancin labari daga majiyoyi na gaskiya kafin su yada shi.

Follow Us