Gwamnatin Katsina Ta Shirya Yaƙi da Rashin Abinci Mai Gina Jiki

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11082025_134810_FB_IMG_1754916355543.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, – 11 ga Agusta, 2025 

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana sabon shirin hadin gwiwa da kulla dabarun bangarori da dama domin magance matsalar rashin abinci mai gina jiki da ke addabar yara da mata a jihar.

Shugaban Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jiha, Dakta Shamsuddin Yahya, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Katsina, inda ya ce rashin abinci mai gina jiki na daga cikin manyan matsalolin lafiyar jama’a, kuma yana daga cikin manyan dalilan mutuwa da rashin lafiya a jihar.

Ya ce rahoton da ƙungiyar Médecins Sans Frontières (MSF) ta fitar kan yawan mace-mace a wata cibiyar kula da yara masu tsananin rashin abinci mai gina jiki, ya zama kira na farga ga kowa maimakon su ɗauke shi a matsayin suka.

“Ba mu dauki rahoton a matsayin korafi ba, sai dai kira ne ga kowa ya hada kai domin magance matsalar, wadda ta samo asali daga dalilai masu zurfi na zamantakewa da tattalin arziki,” in ji shi.

Dakta Yahya ya bayyana cewa, cikin shekaru biyu da suka gabata, gwamnatin Malam Dikko Umar Radda ta bayar da gudummawar kudi ga UNICEF naira miliyan 200 a shekarar 2023 da naira miliyan 300 a shekarar 2024 domin samar da kayan abinci mai gina jiki, wanda UNICEF ta ninka kudin a kowace shekara.

Tun daga shekarar 2016, an raba tallafin naira 250,000 a kowane wata ga kananan hukumomi 14 da aka tantance a matsayin masu matukar bukata, don kula da cibiyoyin warkar da yara a wajen asibiti. Haka kuma, dukkan kananan hukumomi 34 sun rattaba hannu kan yarjejeniya da za su bayar da naira miliyan 1 a kowane wata domin yaƙar matsalar.

A halin yanzu, Katsina na da cibiyoyi 185 na kula da yara a wajen asibiti (OTP) da kuma cibiyoyi 17 na kwantar da marasa lafiya masu tsananin rashin abinci mai gina jiki, inda gwamnati ke kula da fiye da rabin wadannan cibiyoyi.

Ya ce akwai shirye-shirye da dama da gwamnati ke yi wajen samar da abinci, ciki har da rarraba kayan aikin noma, samar da cibiyar injinan noma, da kuma sa ido a kasuwanni domin hana boye abinci.

Sai dai ya bayyana damuwa kan yadda wasu iyaye ke sayar da abincin magani (RUTF) bayan sun karɓa daga cibiyoyi, maimakon su yi amfani da shi wajen warkar da ‘ya’yansu. Don haka gwamnati za ta kafa kotunan tafi-da-gidanka domin hukunta masu laifi da kuma karfafa tsarin kulawa.

Bayan ziyarar Gwamna Radda zuwa cibiyar da rahoton MSF ya nuna yawan mace-mace a watan Yuli, masana daga UNICEF, MSF, ALIMA, World Food Programme, da wasu ma’aikatu sun samar da tsari na bangarori da dama domin yaƙar matsalar, wanda ake jiran amincewar gwamna.

Dakta Yahya ya ce shirin zai shafi bangaren kiwon lafiya da kuma gyaran al’adu, musamman batutuwan tazarar haihuwa da kuma kin amincewa da rigakafin cututtuka, wadanda ke jawo matsalar ta tsananta.

Shima shugaban shirin Accelerating Nutrition Results in Nigeria (ANRiN) a Katsina, Dakta Umar Bello, ya ce shirin ya kai wa fiye da mutane miliyan uku agaji a dukkan mazabu 361 na jihar, ta hanyar ba da Vitamin A, micronutrient powders, iron folic acid, magungunan zazzabin cizon sauro ga mata masu juna biyu, da kuma zinc ga yara masu fama da gudawa.

Ya kara da cewa, sama da ma’aikatan lafiya 1,000 aka horas kan ilimin kiwon lafiyar uwa da jariri, domin wayar da kan iyaye kan muhimmancin shayar da jarirai nono na tsawon watanni shida, fara ciyarwa daidai lokacin da ya dace, da kuma amfani da hanyoyin tazarar haihuwa.

Ya ce a cikin shirin ANRiN 2.0 da zai biyo baya, Katsina za ta ci gaba da matakan rigakafi tare da raba RUTF ga yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki, karkashin tallafin Bankin Duniya, yayin da gwamnati ta ware naira miliyan 700 domin dorewar shirin.

“Gwamna ya kuduri aniyar ci gaba da rigakafi da kuma magance matsalar da ta riga ta faru, tare da hada kai da dukkan masu ruwa da tsaki domin kare lafiyar mata da yara a jihar,” in ji Dakta Bello.

Follow Us