Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Hukumar Kula da Ababen Hawa da Tsaftar Hanya ta Jihar Katsina, wato KASSAROTA, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Babban Darakta na hukumar, Alhaji Dahiru Mani Bagiwa, ta kai ziyarar ban-girma ga Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar Katsina, CP Bello Shehu, domin ƙarfafa haɗin gwiwa a tsakanin hukumomin tsaro da KASSAROTA.
Ziyarar wacce ta gudana a ranar Laraba, 6 ga watan Agusta 2025, ta ba da damar tattauna muhimman batutuwa da suka shafi aikin kiyaye lafiyar hanya da tsaron ababen hawa a fadin jihar Katsina. An mayar da hankali kan yadda jami’an KASSAROTA da na ’yan sanda za su ci gaba da aiki tare domin rage haɗurran hanya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A yayin da yake bayani, Alhaji Dahiru Bagiwa ya bayyana cewa, "’Yan sanda su ne ginshiƙin tsaro a kowace ƙasa. Aiki irin na mu ba zai yi tasiri ba sai da cikakken haɗin gwiwa da su."
Ya ƙara da cewa, "Mun zo ne domin mu tattauna da Mai Girma Kwamishina kan hanyoyin da za mu ƙara inganta ayyukanmu, musamman wajen kare rayuka da lafiyar al’umma a tituna. Hanya na da matuƙar muhimmanci a rayuwar yau da kullum, don haka ba za mu yi biris da hadurran da ke faruwa a cikinta ba."
Da yake zantawa da wakilin Katsina Times, Bagiwa ya jaddada cewa KASSAROTA ba ta da wata matsala da kowace hukuma ta tsaro a jihar, inda ya bayyana cewa akwai kyakkyawar mu'amala da fahimta a tsakaninsu da sauran hukumomi.
A karshe, Bagiwa ya roƙi goyon bayan al’umma, yana mai cewa, “Gwamnati ba ta da niyyar cutar da jama’a. Hukumar KASSAROTA na aiki ne don amfanin jama’a — don kare lafiyar su da dukiyoyin su. A wasu jihohi irin wannan hukuma ta dade da kafuwa, amma a nan Katsina sabuwar ce. In sha Allah za mu ci gaba da wayar da kan jama’a har su fahimci cewa mun zo ne don gyara ba don takura ba.”
Shima da yake tsokaci a wajen ziyarar, Sakataren hukumar KASSAROTA na Jihar Katsina, Al’amin Lawal Batsari, ya bayyana cewa, wannan ziyara na ɗaya daga cikin muhimman ayyukan da hukumar ke aiwatarwa domin ƙarfafa dangantaka da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.
“Wannan aiki na kiyaye hadurra da tsaftar hanya aiki ne na kowa da kowa – direbobi, fasinjoji, jami’an tsaro da ma hukumomin gwamnati baki ɗaya. Ababen hawa wani bangare ne na rayuwar al’umma, don haka yana da matuƙar muhimmanci a kula da lafiyar hanya,” inji shi.
Ziyarar ta samu rakiyar Sakataren hukumar, Al’amin Lawal Batsari; jami’in hulɗa da jama’a na hukumar (PRO), Abubakar Marwana K/Sauri; da kwamandan shiyyar Katsina, Abdurraman Muntari.