Karamar Hukumar Katsina Ta Bai wa Dalibai 96 Tallafin Karatu A KSITM

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29072025_182214_FB_IMG_1753813229171.jpg

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times


Shugaban karamar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya tabbatar da kudirin gwamnatinsa na ci gaba da zuba jari a fannin ilimi ta hanyar bai wa dalibai 96 cikakken tallafin karatu a makarantar koyon fasaha da kirkira ta jihar Katsina (KSITM).

An sanar da hakan ne a wajen bikin kaddamar da tallafin karatun da aka gudanar a dakin taro na KSITM a ranar Talata, 29 ga Yuli, 2025. A wajen taron, an kuma rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tsakanin karamar hukumar da makarantar.

Hon. Miqdad ya bayyana wannan mataki a matsayin wani muhimmin ci gaba da zai amfanar da daliban da kuma al’ummar yankin baki ɗaya.

“Wannan tallafin karatu shaida ce ta yadda muke da yakinin cewa ilimi ginshiƙi ne na cigaban al’umma. Idan muka zuba jari ga matasa, to muna gina makomar Katsina da ma Najeriya gaba ɗaya,” in ji shi.

Ya yabawa daliban da suka ci gajiyar tallafin bisa ƙoƙarinsu da juriya, inda ya ja hankalinsu da su rungumi damar da hannu biyu.

“A hannunku ne burin ku da na iyayenku da kuma burin al’ummarmu gaba ɗaya yake. Ku yi amfani da wannan dama domin ilmantuwa, haɗuwa da juna da kuma jagoranci a gaba,” ya ƙara da cewa.

Shugaban karamar hukumar ya kuma nuna godiya ga iyaye da masu kula da daliban bisa goyon baya da sadaukarwa da suka yi, yana mai cewa hakan ne ginshiƙin nasarar ‘ya’yansu.

Da yake gabatar da sakon gaisuwa a madadin Kwamishinan Ilimi na Jihar Katsina mai kula da manyan makarantu, fasaha da koyon sana’o’i, Alhaji Muhammad Isah Musa, wakilinsa Dikko Bala Kofar Sauri ya bayyana wannan tallafi a matsayin abin koyi wajen ɗorewar cigaban matasa.

“Ina isar da sakon gaisuwar Kwamishina a wannan lokaci mai muhimmanci. Tallafin da shugaban karamar hukumar Katsina ya bayar ga ɗalibai 96 abu ne mai matuƙar tasiri wajen cigaban matasa da gina al’umma,” in ji Bala.

Ya bayyana irin kokarin da gwamnatin jihar ke yi karkashin Gwamna Malam Dikko Umar Radda Ph.D.,CON, wajen dawo da inganci a fannin ilimi, da kuma kawo ƙarshen cibiyoyin karatu marasa rajista da inganci.

“Gwamnatinmu ta kuduri aniyar tabbatar da inganci a manyan makarantunmu. Wannan ya haɗa da tsaftace makarantu masu zaman kansu da wasu cibiyoyin wucin gadi da ke rage darajar ilimi,” in ji shi.

Ya yabawa shugaba Miqdad bisa hangen nesansa da kishinsa ga ilimi, yana mai cewa ilimi shine gado mafi kyau da kowanne shugaba zai iya bari.

“Wannan shiri shaida ne ta yadda shugaban karamar hukumar ke da kishin cigaban matasa da makomar jihar Katsina,” ya ƙara da cewa.

Ya kuma yi kira ga sauran shugabannin kananan hukumomi a fadin jihar da su bi sahu wajen zuba jari a rayuwar matasa ta hanyar tallafin karatu.

Da yake jawo hankalin wadanda suka ci gajiyar tallafin, ya bukaci su dage da karatu tare da mayar da hankali.

“Wannan dama ce mai matuƙar muhimmanci. Ku yi amfani da ita yadda ya kamata, domin nasararku ita ce ginshiƙin cigaban jihar Katsina gaba ɗaya,” in ji shi.

Cikin waɗanda suka halarci taron akwai ɗan majalisar karamar hukumar Katsina, Hon. Aliyu Abubakar Albaba; Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Katsina; Shugaban makarantar KSITM; tsohon mai baiwa Gwamna Masari shawara na musamman, Hon. Tanimu Sada; dalibai, iyaye da sauran baki daga sassa daban-daban.

Wannan bikin ya nuna ƙaruwar haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da cibiyoyin ilimi domin sauƙaƙa samun ilimi ga kowa da kowa da kuma haɓaka cigaban al’umma ta hanyar zuba jari a jari a rayuwar matasan karamar hukumar.

Follow Us