NA ZIYARCI HUBBAREN SAYYADINA ALIYU (A.S) A BIRNIN NAJAF.
- Katsina City News
- 21 Sep, 2023
- 1480
@ Katsina Times
@ Jaridar Taskar Labarai.
Birnin Najaf dake kasar Iraq, Birni ne mai tsohon tarihi na Annabawa, da kuma Musulunci.
Akwai kaburburan Annabawa Allah, hudu a cikin sa. Biyu suna a Makabartar Wadissalam, biyu kuma suna tare da hubbaren kabarin Sayyadina Ali(as) Kanin Manzon Allah (S.A.W) Kuma Mijin Sayyada Fatima (S.A) Diyar Manzon Allah (SAW).
Na ziyarci wannan Hubbaren dake cikin birnin Najaf, a kusan kowane Rana zaku iya iske Dubban mutane Maziyarta.
Hubbaren yana da girma sosai, tsakiyarsa Kabarin Sayyadina Ali (A.S) sai Masallatai da suka kewaye shi, Sai makarantu na Nazarin Addinin Musulunci.
Sai kuma kabarin Annabawa guda biyu. Akwai wajen hutawa kyauta da inda ake amsar Abinci kyauta.
@ www.katsinatimes.com
@ www.jaridartaskarlabarai
07043777779 08057777762