Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa gwamnonin jihohi 18 masu ci a halin yanzu suna karkashin binciken hukumar kan zargin rashawa.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a Legas a ranar Juma’a yayin wani taron wayar da kai game da illolin lalata Naira da kuma yin amfani da ita ba bisa ka’ida ba.
A cewarsa, hukumar za ta dauki mataki a kan gwamnonin bayan karewar wa’adin mulkinsu.
Shugaban EFCC ya bayar da labarin yadda aka kama tsohon gwamna a Burtaniya yana watsar da fam a wani otal.
Ya ce tsohon gwamnan ya tsere daga Najeriya zuwa Burtaniya a rana ta biyu bayan ya mika mulki ga wanda ya gada.
Olukoyede ya ce: “Zan ba ku labarin abin da ya faru a EFCC. A wani lokaci a wannan kasa, muna binciken wani gwamna. Ba muna jira sai sun gama wa’adinsu muke bincike ba.
“A halin yanzu da nake magana da ku, muna binciken gwamnonin jihohi 18 masu ci. Idan suka bar ofis, za mu dauki mataki na gaba.
“Wannan gwamnan an fara bincikensa tun yana kan kujerar mulki. Da ya gama wa’adinsa, washegari ya tsere zuwa Ingila don kaucewa cafke shi da EFCC za ta yi.
“A dai-dai wannan mako kuma, ya kasance bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Ya shirya taron murnar ranar haihuwarsa a otal din da yake zaune.
“Yayin da bikin ke gudana, sai ya fara watsar da fam – takardun fam £50 da £10. Manajan otal din ya samu kiran gaggawa. Da ya sauko ya ga tsohon gwamnan yana watsar da fam din, bai taba ganin irin haka ba a rayuwarsa, sai ya kira lambar gaggawa 911.
“Da jami’an ‘yan sandan Metropolitan suka iso, sai ya roke su da su kama tsohon gwamnan. An kama shi kuma aka yi shirin sanya shi a cikin motar asibiti.
“Mutanen da suka je bikin tare da shi – abokansa, ‘yan uwa da wasu gwamnonin biyu – suka shiga tsakani suka ce tsohon gwamnan ba mahaukaci ba ne, domin manajan otal din ya yi zaton yana da tabin hankali.”
Mun ciro daga shafin
@ daily Nigeria