Katsina Times
Sanata Olubiyi Fadeyi da Francis Fadahunsi daga jihar Osun sun fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), bisa dalilin rikice-rikicen cikin gida da sabani maras mafita da suka dabaibaye jam’iyyar tsawon shekaru. Sai dai sun ki bayyana matakin siyasa da za su dauka na gaba.
Sanata Fadeyi, wanda ke wakiltar Osun ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya sanar da murabus dinsa a wata wasika mai dauke da kwanan wata 12 ga Yuli, 2025, wacce ya aike wa shugaban mazabar PDP ta Ward 3, Oke Ejigbo, Ila Orangun, Osun.
Wasikar na cewa: “Ina mai sanar da ku cewa na fita daga jam'iyyar PDP daga yau. Sabani maras sulhu da rabuwar kai da suka dabaibaye jam’iyyar tare da shari’o’i da suka jawo rarrabuwar kawuna tun bayan shekarun nan uku, sun sa dole na yanke wannan hukunci. Na yanke wannan shawara ne bayan shawarwari da hadin guiwa da abokan siyasa na, iyalina da abokai.”
Haka zalika, Sanata Francis Fadahunsi, wanda ke wakiltar Osun ta Gabas kuma dan majalisa karo na biyu, ya mika wasikar murabus dinsa mai dauke da kwanan wata 12 ga Yuni, 2025, wacce ta bayyana a kafafen sada zumunta a ranar Asabar.
Fadahunsi ya bayyana cewa matsalolin cikin gida da shari’o’i masu tsawo sun hana jam’iyyar daidaituwa tun bayan zaben 2023, lamarin da ya tilasta masa ficewa daga jam’iyyar.
A cikin wasikar da ya aika wa shugaban mazabar PDP ta Ward 4, Fadahunsi ya rubuta: “Ina mai sanar da ku a hukumance cewa na fice daga jam’iyyar PDP daga yau, bisa ga matsalolin cikin gida da rikice-rikice na dindindin da suka mamaye jam’iyyar a matakin kasa bayan zaben 2023. Wannan hukunci ya biyo bayan tuntubar abokan siyasa na, iyalina da abokai.”
Duk da ficewar su daga jam’iyyar, babu daya daga cikin sanatocin da ya bayyana ko za su shiga wata jam’iyya ko kuma matakin siyasa da za su dauka a gaba.