Kwalejin Hassan Usman Katsina Ta Gudanar da Taron Wayar da Kai Kan Aikin Jarida A Wanzar da Zaman Lafiya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes17072025_212642_FB_IMG_1752787516911.jpg

Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times, Alhamis, 17 ga Yuli, 2025

Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina ta gudanar da taron wayar da kai kan Jaridar Wanzar da Zaman Lafiya (Conflict Sensitive Journalism) ga ɗaliban Sashen Kafafen Sadarwa (Mass Communication), a wani bangare na ƙoƙarin kafa zaman lafiya a jihohin da ke fama da rikice-rikice.

Taron, wanda aka gudanar a ranar Alhamis 17 ga Yuli 2025, yana cikin shirin Nigeria–Benin Border Communities Peace Initiative da ke ƙarfafa haɗin gwiwa domin samar da zaman lafiya da tsaro a jihohin Katsina, Kebbi, Zamfara, Sokoto da Neja.

An shirya taron ne ta hanyar haɗin gwiwar Common Ground Journalists Forum, Katsina State, da hadin guiwar ƙungiyar Search for Common Ground, tare da goyon bayan wasu kungiyoyin ƙasa da ƙasa da ke aiki a fannin zaman lafiya da yaɗa sahihan labarai.

Shugaban sashen Mass Communication na kwalejin, a jawabinsa na bude taron, ya jaddada cewa taron ya zo a lokacin da ya dace. Ya nanata cewa ‘yan jarida na da rawar gani a kowanne yanayi na rikici.

“Ko sun sani ko ba su sani ba, ‘yan jarida na cikin masu taka rawa a rikice-rikicen da ke faruwa. Su ne idon al’umma da ke lura da gwamnati da zamantakewa, kuma labaran da suke bayarwa suna iya sauya fahimtar jama’a,” in ji shi.

Alhaji Abdulhamid Sabo, kwararren ɗan jarida kuma Manajan Darakta na Gram FM Katsina, ya yi bayani mai zurfi kan bambanci tsakanin rikici da tashin hankali, inda ya ja hankalin ɗalibai su fahimci tushen rigingimu kafin su wallafa rahotanni.

“Rikici na iya kasancewa tsakanin mutane biyu kacal, amma tashin hankali yawanci yana fitowa daga ƙungiyoyi masu niyyar ɗaukar fansa. Labaran da ku ‘yan jarida ke wallafawa na iya magance matsala ko kuma haifar da wata sabuwa,” in ji shi.

Tijjani Muhammad daga jaridar Daily Trust shi ma ya gabatar da darasi kan yadda ɗan jarida ya kamata ya dinga amfani da harshen da ba na rura wutar rikici ba. Ya bayyana muhimmancin zaɓen kalmomi masu ma’ana da natsuwa.

“Kalmomin da muke amfani da su suna da tasiri. ‘Yan jarida ne ke rubuta sahihin tarihin farko na duk wani rikici. Ya kamata mu tambayi kanmu: wannan rahoto zai haifar da zaman lafiya ne ko rikici?”

Ya ƙara da cewa aikin jarida ba na fafutuka ba ne, amma aikin da ke da tushe a ƙa’ida da dabi’a, wanda ke ƙunshe da alhakin bin gaskiya da tabbatar da daidaito a cikin rahotanni.

Wakilan ƙungiyar Search for Common Ground sun bayyana cewa ɗaliban kafafen sadarwa na da matuƙar muhimmanci wajen samar da zaman lafiya a yankunan da ke fama da rikice-rikice kamar jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto Kebbi da Niger 

“Ku ɗaliban Mass Communication ku ne ‘yan jaridar gobe. Kuna da damar da za ku sauya duniya ta hanyar bayar da sahihan labarai daga inda abubuwa ke faruwa, ba wai na jita-jita ba,” in ji ɗaya daga cikin wakilan ƙungiyar.

Taron ya kasance wata dama ta ilmantarwa da faɗakarwa ga matasa masu sha’awar aikin jarida, domin su fahimci rawar da za su taka wajen gina zaman lafiya a cikin al’umma ta hanyar rubuce-rubuce masu inganci da ma’ana.

Shirin yana ci gaba a matsayin wani bangare na aikin samar da zaman lafiya a Arewacin Najeriya tare da goyon bayan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da na cikin gida.

Follow Us