Gwamnatin Jihar Katsina Ta Bukaci Sauye-sauye a Kundin Tsarin Mulki, Taron Jin Ra'ayi da Aka Gudanar a Kaduna

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12072025_192019_FB_IMG_1752346881074.jpg



Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 

Gwamnatin Jihar Katsina ta gabatar da shawarwari masu zurfi da nuni ga bukatar sauya kundin tsarin mulkin ƙasar nan domin inganta dimokuraɗiyya, samar da shugabanci mai tafiya da kowa da kowa, da kuma bai wa jihohi da kananan hukumomi cikakken ‘yancin gudanar da harkokinsu. Wannan na cikin jawabin da ta gabatar a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan sauya kundin tsarin mulki na shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar a Gidan Janar Hassan Usman Katsina, Kaduna, a ranar Asabar, 12 ga Yuni, 2025.

Wacce ta wakilci Gwamna Malam Dikko Umar Radda ita ce Kwamishiniyar Shari’a kuma Babbar Lauya ta Jihar Katsina, Barrista Fadila Dikko, inda ta gabatar da takardar shawarwari da ke bayyana matsayar jihar Katsina a kan batutuwan da suka shafi kundin tsarin mulki da bukatar sauya shi domin dacewa da zamanin da ake ciki.

A jawabin sa na buɗe taron, Shugaban kwamitin sauya kundin tsarin mulki na shiyyar Arewa maso Yamma, Rt. Hon. Madaki Aliyu Sani, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Marasa Rinjin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, ya bayyana a jawabinsa cewa sauya tsarin mulki ba wai kawai gyara takarda ba ne, illa dai sabunta ginin kasa da al'umma.

Ya jaddada cewa kwamitin da yake jagoranta yana duba kudurori 18 da suka shafi fannoni 13, ciki har da: Sauye-sauyen harkokin zabe, Gyaran bangaren shari’a, Karfafa ayyukan majalisa, Tsaron kasa da kafa 'yan sanda na jihohi, Mulki mai amfani da kowa, Rabon kudade (fiscal federalism), Haƙƙin ɗan adam, 'Yancin kananan hukumomi, Sabbin jihohi da ƙananan hukumomi, Matsayin sarakunan gargajiya, Kasa da 'Yan kasa (indigene), Cigaban matasa da mata

Ya kuma kara da cewa tsarin zai bai wa dukkan ‘yan Najeriya dama su bayar da gudummawarsu daga dalibai, shugabannin gargajiya, kungiyoyin fararen hula, mata da matasa.

Abubuwan Da Jihar Katsina Ta Mayar Da Hankali A Kansu

1. Yaye Nauyin Gwamnatin Tarayya da Sabon Tsarin Rabon Kudade
Jihar Katsina ta bukaci a rage cunkuson iko daga gwamnati ta tarayya, a kuma bai wa jihohi da ƙananan hukumomi cikakken iko a fannonin gudanar da rayuwa. Jihar ta ba da sabon tsarin rabon kudade kamar haka:

 Gwamnatin Tarayya: daga 52% zuwa 37%
 Jihohi: daga 36.72% zuwa 31%
Kananan Hukumomi: daga 20.60% zuwa 32%

Ta kuma bukaci tsarin haraji da zai kasance mai adalci da dai-daito, bisa la’akari da albashi da gudunmawar tattalin arziki.

2. Gyaran Zabe da Mulkin Kananan Hukumomi

Jihar ta bukaci a kafa Hukumar Zaben Kananan Hukumomi mai zaman kanta, a tabbatar da sahihancin zabe da warware gardama kafin rantsar da sabbin shugabanni, da kuma daidaita kudin yakin neman zabe.

3. Gyaran Bangaren Shari’a
An bukaci:

Tsarin nada alkalai bisa cancanta da kwarewa
 'Yancin bangaren shari’a daga tsoma bakin siyasa
Isasshen kudi daga: Majalisar Alkalai ta Kasa (NJC), Kwarewa musamman a fannin shari’a. 

4. Ayyukan Majalisa da Kudaden Ayyukan Yankunan Wakilai
Jihar ta nemi a kafa: Asusun Ayyukan Ci Gaban Yankuna, domin bai wa wakilai damar aiwatar da aiyukan da za su amfani al’ummarsu, da kuma tabbatar da lura da aiwatar da kasafin kudi cikin gaskiya.

5. Wakilci da Shigar Mata da Matasa a Mulki
An bukaci:

 A ware akalla kashi 35% na kujerun siyasa da na gwamnati ga mata
 Daidaiton Mata da Maza a shirin raya tattalin arziki
 Shigar da matasa a harkokin yanke shawara da shugabanci

6. Tsaro da Kafa 'Yan Sanda na Jihohi:
Gwamnatin ta goyi bayan kafa ‘yan sanda na jihohi domin inganta tsaro tare da ci gaba da tsaron al’umma inda ta bada misalin (community Watch Corps) wanda Katsina ke aiwatarwa a kananan hukumomi masu fama da rikice-rikice.

7. Karfafa Hukumomin Gwamnati da Yaki da Rashawa
An bukaci:

 Karfafa hukumomin yaki da rashawa
 Ba su 'yanci da isasshen kudi
 Gyaran aikin gwamnati domin inganta tsari da yawan aiki
 Bunkasa ma’aikatan gwamnati, musamman matasa

8. Matsayin Dan Kasa
An nemi a tabbatar da cewa duk dan Najeriya na da ‘yancin zama indigene a kowanne yanki da yake zaune da yake bada gudummawa. An kuma goyi bayan shigar da tsarin citizenship by investment.

9. Kare Haƙƙin Dan Adam da Walwala
Jihar ta goyi bayan cigaba da amfani da Sashe na 12 na tsarin mulki kan yarjejeniyoyin kasa da kasa, da kuma shigar da tanadi na walwalar jama’a, ciki har da kiwon lafiya, ilimi, da gidaje.

10. ‘Yancin Kananan Hukumomi
An bukaci a bai wa kananan hukumomi cikakken iko da kudi da gudanarwa domin su gudanar da ayyukan more rayuwa ba tare da dogaro da jihohi ko gwamnatin tarayya ba.

An jagoranci tawagar Jihar Katsina da ta halarci taron da ke Kaduna karkashin Sanata Ibrahim Ida, shugaban kwamitin sauya kundin tsarin mulki na jihar. Cikinsu akwai:

 Babbar Lauya kuma Kwamishiniyar Shari’a, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Masu ba da shawara kan kananan hukumomi da aikin gwamnati, Wakilan Majalisar Dokoki da kotun jihar, Hon. Justice Sadiq Abdullahi Mahuta (Rtd), Galadiman Katsina, Engr. Ahmad Diddiri Ahmad, Galadiman Daura, Farfesa Sadiq Radda (BUK), Farfesa Binta Dan-Ali (UMYUK), Dr. Abubakar Siddiq (ABU Zaria), Tsoffin Sakatarorin Dindindin Muhammad Lawal Aliyu, A.D. Umar da Suleiman Yakubu Safana, Shugabannin NBA da CSO na jihar Katsina, Ma’aikatan Ma’aikatar Harkokin Gwamnati da Tsaro

Barrista Fadila Dikko ta kammala da yabawa Majalisar Tarayya bisa shirya wannan taro, tare da jaddada cewa Gwamnatin Jihar Katsina za ta ci gaba da ba da gudummawa don ganin an samar da tsarin mulki da ya dace da kowa, ya kunshi gaskiya, adalci, zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

Follow Us