An Daura Auren Diyar Babban Sakataren Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina

 A ranar Asabar, 28 ga watan Yuni, 2025, an gudanar da daurin auren Asma’u Abdullahi Aliyu, diya ga Babban Sakataren....

Katsina City News June 28, 2025  ·  12:00 AM
| 1,147 Views
 
A ranar Asabar, 28 ga watan Yuni, 2025, an gudanar da daurin auren Asma’u Abdullahi Aliyu, diya ga Babban Sakataren Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Aliyu Yar’adua. An gudanar da wannan muhimmin taron daurin Aure a masallacin Juma’a na Banu Commassie da ke unguwar GRA cikin birnin Katsina.

Taron ya samu halartar jiga-jigan gwamnati, 'yan uwa, abokan arziki, da masoya daga sassa daban-daban na jihar. Cikin manyan baki da suka halarci wannan bikin akwai Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, wanda ya bayyana farin cikinsa da kuma fatan alheri ga sabbin ma'auratan.

Baya ga haka, masu taimaka wa Gwamnan Jihar Katsina, shugabanni daga ma'aikatun gwamnati, wakilan kafafen yada labarai da sauran al’umma sun halarci wannan bikin da ya gudana cikin kwanciyar hankali da yanayi na nishadi da addu’o’i.

A jawabinsa na musamman, Alhaji Abdullahi Aliyu Yar’adua ya gode wa dukkan mahalarta bisa nuna kauna da kulawa da suka yi, inda ya roƙi Allah ya sanya albarka a rayuwar sabbin ma’auratan, tare da basu zuriyya ta gari da zaman lafiya a gidansu.

Wannan daurin aure ya kasance wani lokaci mai cike da farin ciki da tarin albarka, inda al'umma suka taya iyalan murna bisa wannan muhimmin mataki na rayuwa da Asma'u Abdullahi Aliyu ta dauka.

Advertisement

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 5 + 7?