...ta kaddamar da manhajar koyar da sana'o'i ta yanar gizo ga 'yan jihar.
Hukumar Kula da kanana da matsakaitan Sana'o'i ta jihar Katsina, KASEDA, a ranar Larabar nan 26 ga Yuni, 2025, ta gudanar da taron 'Ranar Kanana Da Matsakaitan Sana'o'i Ta Duniya' wato 'International MSME Day' a turance, tare da kaddamar da Manhajar Koyon Sana'o'i ta yanar gizo mai suna 'KASEDA Digital Academy' ga 'yan jihar.
An gudanar da bikin ne a babban filin wasa da Muhammadu Dikko da ke birnin, bikin da ya samu baje kolin kanana da matsakaitan sana'o'i daban-daban musamman na wadanda hukumar ta horar a fadin jihar ta Katsina.
Da yake jawabi a matsayinsa na babban bako a taron, gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda ya taya masu matsakaita da kananan sana'o'i na jihar Katsina murnar zagayowar ranar, inda ya bayyana sana'o'in nasu a matsayin masu habaka ci gaban al'umma da bunkasa tattalin arzikinsu.
Gwamna Radda, ya kuma bayyana irin kokarin da gwamnatinsa ta yi kuma take ci gaba yi wajen bunkasa kanana da matsakaitan sana'o'in a fadin jihar, inda ya bayyana irin makudan kudade da gwamnati ta ware wa hukumar ta KASEDA don bayar da lamuni ga masu Sana'o'i a fadin jihar.
"Babu jihar da ta ware irin Kudin da jihar Katsina ta ware domin tallafa wa matasa wajen gudanar da ayyukan sana'o'insu." In ji shi
Ya ce, "Mun yi wannan kokarin ne domin al'umma su samu jari wanda shi ne ke kawo babban cikas wajen ci gaban kanana da matsakaitan sana'o'i a jiharmu da kasarmu baki daya." Ya bayyanar.
A yayin da take gabatar da nata jawabin, shugabar gudanarwar hukumar ta KASEDA, Hajiya Amina Aminu Malumfashi, wadda ta samu Wakilcin mataimakin gwamnan jihar na musamman kan ci gaban kasuwanci, Dr. Babangida Kabir Ruma ya bayyana a matsayin ta murna da farin ciki a gare su, sannan kuma ta yin waiwaye ga irin rawar da hukumar KASEDA ta taka ga farfadowar sana'o'i na masana'antu a jihar, da kuma irin nasararorin da hukimar ta cimmawa cikin shekaru biyu kacal da kafa ta.
Dr. Ruma ya ce, a karkashin shirin 'Gina Makomarka', hukumar KASEDA ta tallafa wa kanana da matsakaitan sana'o'i sama da 8,000 ta hanyar ba su jari, shawarwari da kuma jagoranci.
"Hukumar KASEDA ta taimaka wajen fitar da rancen Naira biliyan 3.4 ba tare da ruwa ba. Ta gudanar da ƙidayar kanana da matsakaitan sana'o'i na farko a jihar, inda ta gano masu kananan sana'o'i sama da 600,000, da kuma gano masu matsakaitan sana’o’i 50,000 a gefen hanya da cikin unguwanni." In ji Ruma.
Ya hakikance cewar, hukumar ta KASEDA ta kuma horar da matasa 3,000 masu sana'ar gyaran mota tare da hadin gwiwar Kungiyar Masu Gyaran Mota ta Ƙasa (NATA), tare da taimaka wa sama da matasa 1,000 su fara kasuwanci ta hanyar jari da shirin "Dasa Harsashi".
Babangida Ruma, ya karkare da cewar, KASEDA ta kuma kaddamar da manhajar koyar da sanana'o'i ta yanar gizo, wadda za ta bada dama ga duk wani dan jihar shiga a horar da shi darussan kasuwanci daban-daban a cikinta.
"Wani babban abin farin ciki, ina mai sanar da manyan bakinmu cewar a hukumance, KASEDA kaddamar da manhajar koyar da sana'o'i ta yanar gizo wadda aka shirya don koyar da Ilimin sana'o'i ta yanar gizo, da za a bayar da horo ga dubban al'ummar jihar katsina domin su shiga tsarin 'digital economy', wanda za a iya rajista da ita a www.kaseda.ng." Ya karkare.
Taron dai ya hada manyan jami'ai daga bangaren zartarwa da majalisa, sarakunan gargajiya, shugabannin kasuwanci, da daruruwan masu sana’o’i daga sassa daban-daban na jihar.