Komawar Madugun Yan Tawayen Najeriya Ojukwu Najeriya 1982

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes18062025_082412_FB_IMG_1750234908668.jpg



A Rana Mai Kamar Ta Yau 18 Ga Watan Yuni 1982 Shugaba yan tawayen Najeriya Ojukwu ya Koma Najeriya Daga Gudun Hijira Da yayi zuwa kasar Ivory Coast. 

Shugaban Najeriya Shehu Aliyu Usman Shagari ya yi wa Ojukwu afuwa a ranar 18 ga Mayu 1982, wanda ya ba shi damar komawa Najeriya a matsayin dan kasa mai zaman kansa. Ojukwu ya Koma shiga Najeriya daga kasar Ivory Coast a ranar 18 ga watan Yuni 1982.

Ojukwu Ya Samu Tabarbar A Matsayin Jarumi Bayan Dawowarsa Daga Gudun Hijra A Kasar Ivory Coast.

Gashinan yana dagawa Jama'a hannu Daga Mercedes Benz kirar S.

A ranar 18 ga Mayu, 1982, Shugaba Shehu Shagari ya yi afuwa a hukumance ga Emeka Odumegwu Ojukwu.

Ojukwu shi ne jagoran rusasshiyar jamhuriyar Biafra. An ruguje Jamhuriyar bayan yakin basasar Najeriya. An kai Ikemba na Nnewi gudun hijira a Ivory Coast (yanzu Cote d'Ivoire).

Ya dawo Najeriya da karfe 11.55 na safe, a ranar 18 ga Yuni, 1982, bayan kimanin shekaru 12 a gudun hijira.

Bayan da ya dawo daga gudun hijira, a Aba, Ojukwu ya samu tarba mai ban sha'awa tare da gaisuwar bindiga 21.

An dawo da shi ne tare da wakilan jam’iyyar NPN mai mutum 11 karkashin jagorancin Dr Chuba Okadigbo. Kafin ya hau jirginsa Boeing 727 daga Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast ya ce: " Lalle Najeriya ta dade."

Daga baya ya koma jam’iyyar NPN, inda ya koma siyasa a hukumance.

Daga shafin Muhammad Cisse 

Follow Us