Wani matashi da aka bayyana sunansa da Kabir Ja’afar, wanda aka fi sani da “Kabir Hisba,” yana fuskantar bincike a garin Malumfashi, Jihar Katsina, kan zargin aikata luwadi da akalla yara maza 14.
Kabir ya shahara a cikin al’umma wajen yada kyawawan dabi’u, tare da kasancewa a matsayin mamba a kungiyar Hisba, wata kungiya da ke sa ido kan bin dokokin tarbiyya da addini. Wannan lamari ya jefa jama’a cikin firgici da tambayoyi kan yadda aka daina tantance masu mukami ko tasiri a cikin al’umma.
Rahotanni sun nuna cewa Kabir yana rike da matsayi mai muhimmanci a Hisbar Malumfashi, wanda hakan ya sa iyaye da yara suka amince da shi, suna barin 'ya'yansu karkashin kulawarsa.
Yayin da wannan zargi ke kara yaduwa a kafafen sada zumunta da cikin al’umma, wasu daga cikin jama’a sun nemi a ware laifin daga kungiyar da ake alakanta shi da ita, suna mai cewa irin wannan barna tana iya faruwa a kowace kungiya ta addini ko jami'an tsaro.
Rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomi sun fara cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin da hanyoyin da wanda ake zargin ya bi wajen samun amincewar iyaye da yaran da ake zargi ya ci zarafinsu.
Masana, al’umma da masu fafutukar kare hakkin yara sun shawarci iyaye, da kuma kungiyoyin al’umma da su zamo masu tsananin kula da wadanda suke ba da damar kulawa da yara. Sun ce yana da muhimmanci a rika binciken tarihi da hali na masu tasiri a al’umma, komai kima da suna da suke da shi.
Wannan rahoto ya samo asali daga Danjarida Malam Kabir Yahuza Malumfashi.