Daga Wakilanmu
Al'ummar garin Gora II da ke ƙaramar hukumar Safana a jihar Katsina, sun koka a kan yadda aka ɗauke sojojin da ke ba su kariya tun shekarar 2020.
Mutanen da jaridun Katsina Times suka tattauna da su, sun bayyana cewa, sojojin da aka ɗauke tun 9/5/2025 suna zaune ne a makarantar Sakandare da ke garin.
Suka ce sojojin suna ba garin Gora II kariya da kuma sama da garuruwa 20 da ke kusa da garin.
Daga cikin garuruwan akwai Maikada, 'Yar Lilo, Makaurachi, Ganuwa, Guzurawa da sauransu.
Mutanen suka ce sojojin kuma suna ba da kariya ga makaranta ɗaya tilo da a nan ake duk karatun boko da ake yi a yankin.
Mutanen suka ce, sojojin suna ba kasuwar Gora II kariya, wadda ita ce babbar kasuwa a baki ɗayan yankin Safana.
Mutanen garin na Gora II suka ce kariyar da suke samu daga sojoji ta sa duk shekara noman da suke yi yana amfanar yankin baki ɗaya da ma jihar ta Katsina.
Mutanen suka ce a tsawon zaman da sojojin suka yi tun daga farkon zuwan su a shekarar 2020 zuwa lokacin da aka ɗauke su 9/5/2025, mutanen garin na zaman lafiya da haɗin kai ga duk rukunin sojan da aka kawo.
Mutanen suka ce, sam ba su taɓa samun wata matsala da sojojin da ake kawo a duk tsawon zaman su ba.
Mutanen suka ce, suna roƙo da kira ga mai girma Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa PhD da ya sanya baki.
Suka ce, ana ɗauke sojojin yanzu ɓarayin daji har sun fara addabar duk ƙauyukan da suka ɗau shekaru cikin aminci da kwanciyar hankali.
Mutanen suka ce, ɓarayin na daji sun shigo har makarantar da ke garin, wadda a da nan ne mazaunin sojojin, kuma ake karantarwa sun fara kwashe kayanta.
Suka ce ɓarayin sun kuma hana karatun daga ƙauyukan da ke zuwa Gora II makaranta.
Mutanen suka ce ɓarayin har sun fara shigowa garin na Gora II suna sace-sace.
Mutanen suka ce, sun kai kukan su har a Majalisar Dokokin Ƙasa, wanda Ɗan Majalisarsu ya kai ƙorafin, amma har yanzu ba abin da ya canza.
Jaridun Katsina Times sun tuntuɓe Kwamishinan Tsaro na jihar Katsina, Alhaji Nasiru Mu'azu Ɗanmusa, wanda ya ce ofishinsa ya san da maganar da kuma matsalar.
Ya ce, "Shugaban ƙaramar hukumar Safana da Ɗan Majalisar Dokokin Jiha daga Safana da Yariman Safana duk sun kawo wannan koke."
Kwamishinan Tsaron ya ƙara da cewa sojoji suna ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya ne, kuma ƙwararru ne, aikinsu yana da tsari.
Kwamishinan ya ce, "Mun samu Kwamandan na sojojin da ke kula da yankin Katsina, inda ya bayyana cewa ba da son ransu suka ɗauke sojojin da ke Gora II ba. Ya ce suna da tsarin tafiyar da aikinsu bisa ƙwarewa yadda za su iya ba mutane kariya. A kan haka suka matsar da sojan Gora II zuwa 'Yar Malamai."
Kwamishinan Tsaro ya ƙara da cewa, ƙarancin sojan na daga dalilan da kan sanya a rufe wani sansanin soja a ƙara wa wani ƙarfi.
Ɗanmusa ya tabbatar wa da jaridun Katsina Times cewa in har jihar Katsina ta samu ƙarin soja garin Gora II na cikin inda za a yi la'akari da shi.
Binciken Katsina Times ya gano mutumin da zai iya tasiri ga ƙarin soja a Katsina shi ne Sanata Abdul'aziz Musa 'Yar'adua, Sanata mai wakiltar katsina ta Tsakiya, kuma shi ne Shugaban Kwamitin Harkokin Soja a Majalisa.
Mun yi ta ƙoƙarin jin ta bakin Sanata Audu Soja a kan matsalar Gora II, amma haƙar mu ba ta cimma ruwa ba.
Mun kira wayarsa, mun aika masa saƙon rubutu duk ba amsa.