Shugabar Ilimin Manya ta Katsina Ta Kai Ziyarar Aiki A Cibiyoyin Karatu A Kananan Hukumomi 4.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28052025_011118_FB_IMG_1748394602588.jpg

...Ta ziyarci Cibiyoyin karatu a garin da ke da barazanar tsaro don duba Ilimin Manya.

Daga Auwal Isah Musa | Katsina TIMES 

A ci gaba da ziyarar aiki wadda Sakatariyar Zartarwa ta Hukumar Ilimin Manya ta Jihar Katsina, Hajiya Bilkisu Muhammad Kaikai ke yi, ta sake kai wata ziyarar aiki ga Makarantun Tsangayoyi, Cibiyoyin koyon karatu na yaki da jahilci da koyar da sana'o'i a Kananan Hukumomin Dutsin-ma, Kankiya, Kusada da Ingawa.

Ziyarar wadda ta hada da garin da ke da barazanar tsaro mai suna 'yarkutungu da ke a karamar hukumar Kankiya wanda a haka ake koyar da Ilimin yaki da jahilci ga Matan garin sama da 100, an gudanar da jerin ziyarar a ranar Laraba 27 ga Mayu 2025.

A yayin ziyarar, Hajiya Kaikai ta bayyana wa daukacin cibiyoyi da Makarantun Tsangayoyin da ta ziyarta cewar, Ziyarar ta gani da ido ce tare da karfafa gwiwar malamai da dalibai da duba yanayin yadda ake gudanar da karatu domin tabbatar da kwalliya na biyan kudin sabulu a matsayinta na shugaba a hukumar don sauke hakkin da aka dora mata.

Hakazalika ta kuma jaddada irin kudirin da gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Radda yake da shi na yaki da jahilci tare da taimaka wa jama'ar jihar ta hanyar samar da ilimi da horo na sana'o'i domin dogaro da kai.

A cewarta, wannan na daga cikin irin cikin tsare-tsaren gwamnan wanda hukumar da take shugabanci take aiwatarwa tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar, don ganin an bunkasa ilimin manya da kuma karfafa makarantun Tsangaya a fadin jihar.

Hajiya Kaikai ta bayyana jin dadinta a daukacin Tsangayoyi da cibiyoyin da ta ziyarta, inda ta yaba masu kan yadda Malamai da Dalibai ke nuna jajircewa da kuma fahimtar karatuttukan da ake koyar da su; biyo bayan gwajin da ta yi masu a ziyarar, inda ta yaba da kokarinsu matuka.

Da suke maida jawabi, daukacin Malaman cibiyoyin da na Tsanyayoyin da aka ziyarta, shugabannin kananan hukumomi da na sarakunan gargajiya sun bayyana farin cikinsu bisa ga yadda aka farfado da makarantun yaki da jahilci da na Tsangayoyi bayan dogon barcin da suka yi, inda suka yaba wa shugabancin Hajiya Kaikai bisa ga raya wadannan fannoni, har ma suka bayyana cewar gwamna Radda ya aje kwarya a gurbin da ya dace da ita, domin har sun fara ganin alfanun wannan karatu ga al'ummominsu, inda suka yi addu'ar samun nasarar ayyukan hukumar da kudurorin gwamnan jihar.

Makarantun Tsangayoyi, Cibiyoyin Koyon Sana'o'i da Makarantun Yaki da jahilcin da aka ziyarta sun hada da: Makarantar Yaki da jahilci ta Manya mata a gidan Hakimi, Makarantun Tsangayoyi biyu da makarantar koyo Sana'o'i ta Mata a Dutsin-ma; Makarantar Tsangaya ta yara da Makarantar Yaki da Jahilci ta mata a garin Yarkutungu a Kafin-soli; Makarantar yaki da jahilci ta Maza a kofar gidan Hakimi a Kankiya; Makarantar Tsangaya ta yara da ta yaki da jahilci ta Mata da ta koyon Sana'o'i ta mata a Kusada; da kuma Makarantar tsangayoyi biyu ta yara a Ingawa.

Bugu da kari, a yayin ziyarar, Hajiya Bilkisu Kaikai da tawagarta sun ziyarci iyayen kasa da shugannin mulki na kanann hukumomin, daga cikinsu akwai: 'Yandakan Katsina Hakimin Dutsin-ma Alhaji Sada Muhammad Sada, Kankiyan Katsina Alhaji Musa Hassan Sada, Shugaban Karamar Humar Kusada Honorabul Sani Aminu Dangamau, Wakilin Bebeji Galadiman Kusada, Alhaji Ibrahim Galadima da sauransu.

Follow Us