A ranar 21 May 2025 aka yi gagarumin taron jam'iyyar APC na ƙasa taron da aka watsa shi kai tsaye a wasu kafofin watsa labarai na talabijin, redio da yanar gizo.
A taron, an yi abubuwa da yawa daga cikinsu har yadda wasu ministoci suka bayyana irin nasarorin da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta samu a cikin shekaru biyu.
Daga cikin abun da aka yi akwai nishadantarwa, wanda ya haɗa da kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe.
Babban wanda ya ɗauke hankalin kowa a taron shi ne mawaƙin nan mai suna Dauda Kahutu Rarara.
Ya yi waƙen nan nasa har da wadda ya yi da aka rubuta masa, kuma ya haddace da yaren Tinubu na Yarbanci.
Bayan ya kammala waƙen ne sai Rarara ya nufo kai tsaye wajen shugaba Tinubu domin su gaisa.
Kamar yadda duniya ta gani a kwatunan talabijin da shafukan sada zumunta, Rarara na tunkaro Tinubu don su gaisa, sai kawai Shugaban ƙasa ya miƙe tsaye domin su gaisa da Rarara.
Ya Subhanallahi! Wannan lamari da me ya yi kama, kuma ya za a fassara shi?
Waye Rarara da har Shugaban Tarayyar Nijeriya zai miƙe wa tsaye don ya tunkaro shi su gaisa?
Sunan sa Dauda Kahutu laƙabinsa Rarara, yana da miƙidarin shekaru 43 zuwa 45.
Ya fara makarantar Firamare daga bai ƙara shiga ajin boko ba. Sai aka turo shi Kano karatun Allo. Daga karatun Allo ya faɗa waƙar siyasa.
Waƙoƙinsa suna daga yabo ne zuwa habaici da zambo. Yana iya yabon ka yau, kuma gobe ya yi maka habaici da zambo. Misalan waƙen Kwankwasiyya da kuma waƙen Tsula ya tsallake, da misalin waƙoƙin yabon da ya yi wa tsohon shugaban ƙasa Buhari da kuma taron manema labarai da ya yi a Kano yana jadadda cewa duk matsalar da ƙasar nan ta shiga mulkin Buhari suka jawo shi.
Waye shugaba Tinubu? Yana da shekaru sama da saba'in a duniya. Hamshaƙin Attajiri ne, wanda ya taka rawa wajen gwagwarmayar dawo da dimokaraɗiyya a Nijeriya, tsohon Sanata, tsohon Gwamnan Legas har karo na biyu, wanda turbar da ɗora jihar Legas bisa shi take tafiya, yanzu kuma Shugaban Tarayya Njeriya, ɗaya daga cikin ƙasashe masu girma da tasiri a duniya.
A waƙar Rarara da ya rera a ranar bukin APC a fadar shugaban waɗanne baitoci ne suka ratsa shi har ya miƙe wa mawaƙin yabo, habaici da zambo kamar Rarara?
Wani abin takaici a ranar, ganin yadda shugaban ƙasa ya miƙe tsaye ga Rarara duk wani a ɗakin taron, tun daga mataimakin shugaban ƙasa, shugaban jam'iyya zuwa ministoci. Haba! A kan me?
Kirari ne fa da yabo Rarara ya yi wa shugaban ƙasa, ba wata addu'a ko nasiha mai hujjar ilmi ya yi masa ba. Ba kuma jawo hankalinsa ya yi ba wanda har ya ratsa masa zuciya ya yi ba.
Me wannan ke nufi idan kirari da yabo za su iya yi wa shugaban ƙasarmu tasiri har ya miƙe wa mawaƙi tsaye a gaban duniya?
Tsakaninka da mawaƙi, kyauta da godiya komai ya faɗa maka shi ne abun da aka sani, sai kuma yi masa hidima a lokacin buƙatarsa tun da mawaƙinka ne.
Malamai, masana ko iyayen ƙasa, ko waɗanda suka yi wata sadaukarwa ga ƙasa sune aka sani ana miƙe masu don girmamawa.
A nan a kuma ra'ayin jaridun Katsina Times Gaskiya shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kwafsa.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
07043777779 08057777762