...Malaman Sun Yi Godiya Ga Gwamnan Katsina
Daga Wakilanmu
Malamai a Hukumar Ilmin Firamare ta ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina, sun yi godiya ga Gwamna Malam Umar Raɗɗa da Hukumar Kula da Makarantun Firamare ta jihar Katsina (SUPEB) a kan matakin gaggawa da aka ɗauka na kafa kwamiti mai ƙarfi don binciken zargin da aka buga a jaridun Katsina Times a wani labarin su mai taken 'Bincike na Musamman: Zarge-Zarge a Hukumar Ilmi ta ƙaramar hukumar Bakori.'
Malaman da suka yi magana da jaridun Katsina Times, sun yi jinjina ta musamman ga kwamitin Hukumar SUPEB da ke ƙarƙashin jagorancin Honourable Rabi'u Idris da masu mara masa baya su huɗu.
Malaman sun ce kwamitin ya nuna dattaku da kuma adalci da kiran duk wani mai ƙorafi ya zo ya bayyana ƙorafi da hujjojinsa ba tare da wani takura, tauye haƙƙi ko barazana ba.
Malaman sun ce, zaman da aka yi a buɗe, kuma a yanayi mai kyau ya ba da nasarori masu yawan gaske.
A taron an gano cewa wasu ƙorafe-ƙorafen da suka bayyana wa jaridun Katsina Times akwai rashin fahimta da kuma rashin neman bayani ingantacce daga inda ya kamata su samu bayanin da za ka fahimta.
A taron an gano duk waɗanda akan cire wa kuɗi ana cire wa ne sakamakon wani bashi da ke kan su ba su kammala biya ba, ko kuma a cire masu fiye da abin da ake bin su bashi.
Kwamitin ya ce duk inda aka samu irin wannan matsala, to Malami ya garzaya SUPEB da hujjojinsa na takardu.
A zaman an ce ba wanda ya isa ya tsayar maka da albashi babu dalili, shi ma in ka ga shiru kar ka tsaya Bakori kana mita, garzaya SUPEB da hujjojinka.
Shugaban kwamitin binciken ya jadadda cewa, "Duk wanda ya ce ka kawo Taro saboda ƙarin girma, wanda ka cancanta, garzayo SUPEB ka kawo bayani da hujjojinka, za ka ga yadda za a yi da shi".
Zaman kwamitin binciken da Malaman Bakori ya zama wani taro na wayar da kan juna da fahimtar aiki.