Daga Wakilin Mu
Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Kurfi da Dutsinma a Jihar Katsina, Hon. Aminu Balele Dan Arewa, ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’umma da iyalan wadanda suka rasa rayukansu a sakamakon hare-haren da ’yan bindiga suka kai a wasu sassan kananan hukumomin Kurfi da Dutsinma.
Ziyarar ta gudana ne da yammacin ranar Lahadi, 25 ga watan Mayu, 2025, inda Dan Majalisar tare da wasu jiga-jigan tafiyarsa suka kai ziyara a garuruwan Kurfi, Dutsinma, Sabon Layi da Barci domin jajanta wa iyalan mamatan da kuma duba halin da wadanda suka tsira daga harin suke ciki.
Hon. Aminu Balele ya bayyana alhinin sa da kuma kaduwar zuciyarsa kan yadda rayuka ke salwanta a yankin sakamakon rashin tsaro. Ya ce lokaci ya yi da za a tashi tsaye domin karfafa gwiwar al’umma da kuma daukar matakan magance wannan matsala da ta addabi yankunan karkara.
A yayin ziyarar, Dan Majalisar ya mika sakon ta’aziyya da jaje ga iyayen gida da dangin mamatan, inda ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya jikan mamatan da rahama, ya kuma baiwa wadanda suka rasa dangi da dukiyoyinsu hakurin jure wannan musiba.
Bugu da kari, ya yi addu’ar samun dawwamammen zaman lafiya da daukewar hare-haren da ke ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.
Hon. Aminu Balele ya kuma tabbatar da kudirinsa na ci gaba da aiki tare da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an shawo kan matsalar tsaro a yankin. Ya bukaci jama’a da su ci gaba da baiwa jami’an tsaro hadin kai da goyon baya domin samar da ingantacciyar tsaro a al’umma.
Ziyarar ta kasance mai daukar hankali kuma ta kara wa al’umma kwarin gwiwa, inda da dama daga cikinsu suka nuna godiya ga Dan Majalisar bisa wannan ziyara da kuma kulawar da yake nunawa ga yankin da ya ke wakilta.