Daga Wakilin mu - Kurfi
Limamai, ladanai da matasan da ke amfani da kafafen sada zumunta daga kananan hukumomin Kurfi da Dutsinma a jihar Katsina sun bayyana cikakken goyon bayansu ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, domin sake tsayawa takara a zaben 2027.
Wannan matsaya ta fito ne a wani taron musamman da aka gudanar a ranar Lahadi, 25 ga watan Mayu, 2025, a gidan dan majalisar tarayya mai wakiltar Kurfi da Dutsinma, Hon. Aminu Balele Dan Arewa, a karamar hukumar Kurfi.
Hon. Dan Arewa ya bayyana cewa goyon bayan da limamai da ladanai da matasan suka nuna, wani babban alamar karbuwa ne ga Gwamna Radda a tsakanin al’umma. Ya ce tuni ya sanar da gwamnan cewa kananan hukumomin sun amince dareshin ya zama ɗan takarar APC guda ɗaya a zaben 2027.
"A matsayinmu na wakilan jama'a, mun zauna tare da ‘yan majalisa 18 a Abuja domin jaddada matsayar mu ta marawa Gwamna Radda baya dari bisa dari," inji Dan Arewa.
Taron ya zama dama ga mahalarta wajen mika koke-koke da shawarwari ga dan majalisar, wanda ya tabbatar musu da ci gaba da karɓar ra’ayoyinsu. Haka kuma, ya basu alawus kamar yadda ya saba a kowane wata.
Mahalarta taron sun bayyana kudirinsu na ci gaba da marawa Gwamna Radda da Hon. Dan Arewa baya, tare da alkawarin amfani da kafafen sada zumunta domin yada manufofi da nasarorin gwamnati.