Daga Zaharaddeen Ishq Abubakar | Katsina TIMES 22 Mayu, 2025
Gwamnatin Jihar Katsina ta sake tabbatar da goyon bayanta ga Hukumar Kiyaye Hadurran ta Ƙasa (FRSC) domin ƙara inganta matakan tsaron hanyoyi a faɗin jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar (SGS), Alhaji Abdullahi Garba Faskari, ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ban girma da sabon Kwamandan Sashen FRSC na Jihar Katsina, Kwamandan Maxwell Kaltungo Lede, ya kai masa a ofishinsa da ke Cibiyar Ma’aikatun Gwamnati, ranar Alhamis, 22 ga Mayu, 2025.
A madadin Gwamna Malam Dikko Umar Radda Ph.D Sakataren ya yi maraba da sabon kwamandan tare da bayyana godiyarsa bisa hangen nesansa da ƙwarewar da ya zo da ita. Ya ce sabbin tsare-tsare da dabarun da Kwamanda Lede ya gabatar—musamman shirin matakin duniya da fasahar wayar hannu—sun zo a kan kari, kuma za su taimaka gaya wajen ƙara tsaro da rage haɗurra a titunan jihar.
“Ko da yake FRSC hukuma ce ta tarayya, al’ummar Jihar Katsina ne kai tsaye ke cin gajiyar ayyukanku. Don haka, muna kallon aikin ku a matsayin wani ɓangare na ci gaban jiharmu. Za mu ci gaba da haɗin gwiwa da ku don tabbatar da nasarar shirin tsaron hanya,” in ji Faskari.
Sakataren ya karɓi shirin samar da tsarin aiki da hannu bibbiyu, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da shiga ayyuka tare da hukumar don rage yawaitar haɗurra da kuma inganta bin dokokin hanya. Ya ba Kwamanda Lede tabbacin goyon bayan gwamnatin Gwamna Radda a kowane lokaci.
A nasa jawabin, Kwamandan hukumar Kiyaye Hadurra FRSC, Maxwell Lede, ya nuna godiyarsa ga SGS da al’ummar Katsina bisa tarbar da aka masa tun zuwansa a ranar 4 ga Mayu, 2025. Ya bayyana cewa tsaron hanya matsala ce ta lafiyar jama’a a duniya, inda ya nuna kudurin Najeriya na rage mutuwa sakamakon haɗurran hanya da kaso 50% kafin shekarar 2030, kamar yadda ake bukata a manufofin cigaban duniya na Majalisar Ɗinkin Duniya (SDG 3.6).
Kwamanda Lede ya jinjinawa wanda ya gada, bisa gagarumin aikin da ya fara, tare da bayyana shirin sa na farfaɗo da Majalisar Tuntuba kan Tsaron Hanya ta Jihar Katsina da kuma shimfiɗa ta zuwa matakin ƙananan hukumomi kamar yadda gwamnatin tarayya ta tanada.
“Katsina na da dukkanin damar da ake buƙata don zama abar koyi a tsaron hanya, ba kawai a Najeriya ba har ma da nahiyar Afirka baki ɗaya. Abin da ake buƙata yanzu shi ne ƙarfin gwiwar siyasa da haɗin kai da masu ruwa da tsaki,” in ji shi.
Yayin da yake bayyana wasu sabbin dabaru, Kwamandan ya gabatar da sabuwar Manhajar Wayar FRSC, wadda ke bai wa jama’a damar samun agajin gaggawa, tantance lasisin tuƙi, gano wuraren haɗurra da kuma bibiyar ayyukan jami’an tsaron hanya. Ya ce manhajar za ta ƙara buɗe kofar fahimta da haɗin kai tsakanin jama’a da hukumar.
“Manhajar na bai wa jama’a dama su kai ƙorafi, su duba sahihancin rajistar motoci da kuma taka rawa wajen tabbatar da amincin amfani da hanyoyi,” Lede ya bayyana.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, manyan jami’an hukumar Kiyaye Hadurra FRSC daga Shiyyar Jihar Katsina.
Ziyarar ta nuna sabuwar dangantaka mai ƙarfi tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da Hukumar Kiyaye Hadurra FRSC, wadda ke da nufin samar da hanyoyi masu aminci da ingantaccen tsarin sufuri ga kowa da kowa a fadin jihar.