Lalacewar Magudanar Ruwa a Ƙerau cikin Birnin Katsina na Barazana ga Dukiya da Lafiyar Jama’a

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09052025_201624_FB_IMG_1746821732826.jpg



Daga Abdulrazaq Ahamed Jibiya 

Mutane mazauna unguwar Ƙerau da ke cikin birnin Katsina na fuskantar barazana ga rayuwarsu sakamakon mummunar lalacewar wata tsohuwar magudanar ruwa da ke yankin, wadda aka gina kimanin shekaru 50 da suka wuce.

Rahotanni sun bayyana cewa magudanar ruwan na ci gaba da tabarbarewa, lamarin da ke barazana ga gidajen da ke kusa da ita, musamman a lokacin damina. Mazauna yankin sun bayyana damuwarsu kan yadda zaizayar ƙasa ke ci gaba da lalata muhallin su, inda suka ce matsalar ta wuce ƙarfin su na magancewa.

Wasu daga cikin mazauna yankin, ciki har da Alhaji Yusuf Dankano da Alhaji Musa Jikamshi, sun ce sun shafe shekaru suna kai ƙorafi ga hukumomi, amma ba a ɗauki matakin da ya dace ba. A cewarsu, lalacewar magudanar ruwan na barazana ga lafiyar jama’a sakamakon yaduwar sauro da wasu ƙwari da ke haifar da cututtuka.

Umar Abubakar da Habibu Ahmed Dara sun bayyana cewa yankin ya zama matattarar sauro da sauran ƙwari masu haddasa cututtuka, musamman ga yara da tsofaffi. Haka zalika, wata mata mai suna Rabi’atu Ahmed Danbaba ta bayyana damuwarta kan yadda matsalar ke shafar lafiyar yara, inda ta gargadi cewa idan ba a dauki matakin gyara ba kafin damina mai zuwa, matsalar za ta ƙara muni.

Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin gwamnati da su gaggauta ɗaukar matakin gina sabuwar magudanar ruwa domin ceto rayukan al’umma. Sun bukaci hadin gwiwar wakilan da ke wakiltar yankin domin kawo mafita ga matsalar da ta dade tana addabar Ƙerau.

Masu sharhi sun bayyana cewa irin wannan matsala na buƙatar matakin gaggawa daga gwamnati domin dakile haɗurra da kare lafiyar jama’a, musamman a yanayi na sauyin yanayi da ake fuskanta a yanzu. Sun kuma bukaci samar da tallafi ga waɗanda wannan matsala ta shafa kai tsaye.

Follow Us