Daga Ibrahim Mohammed Gupa Jnr. – Etsu Gupa Abawa I, Jami’in Yaɗa Labarai
Gwamnatin Kwalejin Bida da ke Jihar Neja, wadda aka kafa tun shekarar 1912 a matsayin Makarantar Sakandare ta Ƙaramar Hukuma (Provincial Secondary School), ta kasance daya daga cikin manyan cibiyoyin da suka bayar da gagarumar gudummawa wajen gina shugabanni a tarihin Najeriya.
Sai dai abin mamaki da ban al'ajabi shi ne irin ci gaban da ɗaliban zangon 1957 zuwa 1962 suka samu. Daga cikin dalibai 24 da suka kammala a wannan lokaci, an samu:
Janar Ibrahim Badamasi Babangida (Lamba 9) – Ya zama Shugaban Ƙasa na mulkin soja daga 1985 zuwa 1993.
Janar Abdulsalami Abubakar (Lamba 16) – Shugaban ƙasa daga 1998 zuwa 1999, wanda ya mika mulki ga gwamnatin farar hula.
Janar Gado Nasko (Lamba 21) – Gwamnan Jihar Sokoto.
Janar Garba Duba (Lamba 10) – Gwamnan Jihohin Bauchi da Sokoto.
Kanal Sani Bello (Lamba 13) – Gwamnan Jihar Kano.
Janar Mohammed Magoro (Lamba 3) – Ministan Harkokin Cikin Gida a zamanin Janar Buhari.
Brigadier Mohammed Sani Sami (Lamba 23) – Gwamnan Bauchi (1984–1985), yanzu sarki mai daraja a matsayin Sarkin Zuru.
Janar Mamman Vatsa (Lamba 6) – Ministan Birnin Tarayya (FCT), wanda daga bisani aka yanke masa hukuncin kisa a 1986 bisa zargin yunkurin juyin mulki a zamanin shugabancin abokinsa Janar Babangida.
A fannin ilimi kuwa, an haifi fitattun malamai da masana da suka fito daga wannan makaranta irin su:
Makarantar ta kuma haifar da sarakuna kamar:
Zangon 1957 zuwa 1962 na Gwamnatin Kwalejin Bida wani gagarumin tarihi ne da ba za a manta da shi ba a tarihin Najeriya. Daga ɗalibai 24 kawai, aka samu shugabanni masu rinjaye a fannoni daban-daban na rayuwa – soja, shari’a, siyasa, jakadanci, da sarauta – abinda ke nuna muhimmancin ilimi da tasirin da irin wannan makaranta ke da shi wajen gina ƙasa.