Ƴanmajalisar Dattawan Najeriya uku na babbar jam'iyyar hamayya ta PDP daga jihar Kebbi za su sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya tabbatar.
Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka ne ga manema labarai, jim kaɗan bayan ganawar sanatocin da Shugaba Tinubu a fadarsa da ke Villa.
''Sanatocin jam'iyyar PDP daga jihar Kebbi a yau sun tabbatar wa shugaban ƙasa cewa sun fice daga jam'iyyarsu ta PDP tare da dawo jam'iyarmu ta APC'', in ji Ganduje.
Abdullahi Ganduje ya ce sanatocin uku za su bayyana wa majalisar dattawa matsayar tasu a mako mai zuwa kamar yadda kundin tsarin ƙasar ya tanadar.
Sanatocin uku sun haɗa da Sanata Adamu Aliero da Sanata Yahaya Abubakar Abdullahi da kuma Sanata Garba Maidoki.
A baya-bayan nan batun sauya sheƙa tsakanin manyan ƴansiyasa na ci gaba da ɗaukar hankali a ƙasar, bayan da wasu jiga-jigan jam'iyun hamayya ke komawa APC mai mulki.
Ko a makonnin baya ma gwamnan jihar Delta da tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa - wanda shi ne ya yi wa PDP takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023 - suka sanar da komawa APC.
BBC Hausa