Jihar Katsina Ta Kafa Sabon Sashen Harkokin Banki da Kudi Don Taimakawa Ci Gaban Tattalin Arziki

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29042025_151933_FB_IMG_1745939893380.jpg


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times. Talata, 29 ga Afrilu, 2025 — 

A wani muhimmin taro da aka gudanar a Otal ɗin Alhujrat da ke cikin garin Katsina, gwamnatin Jihar Katsina ta kafa sabuwar alakar haɗin guiwa tsakanin bankunan kasuwanci da gwamnatin jiha, domin ƙarfafa hadin kai da bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Taron, wanda ya samu halartar manyan daraktoci da shugabannin bankunan kasuwanci a jihar, ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Hajiya Bilkisu Suleman Ibrahim, mai bai wa Gwamna shawara ta musamman kan harkokin Banki da Kudi.

A cikin jawabinta, Hajiya Bilkisu ta bayyana cewa an kafa sabon Sashen Harkokin Banki da Kudi ne domin ya kula da dukkan harkokin da suka shafi banki a gwamnatin jihar Katsina. Ta ce wannan sashe zai rika zama hanyar sadarwa tsakanin bankunan kasuwanci da gwamnatin jiha.

“Bankunan kasuwanci na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arziki, kuma muna da buƙatar ƙarfafa alaƙar aiki da su. Saboda haka, wannan sashe zai kasance hanyar da duk wata mu’amala ko korafi tsakanin gwamnati da banki zai bi,” in ji ta.

Hajiya Bilkisu ta bayyana fa’idodin wannan haɗin gwiwa kamar, Inganta ilimin kuɗi da haɗa al’umma da tsarin kudi musamman a yankunan da ba su da cikakken isasshen samun damar shiga banki. Taimaka wa ƙanana da matsakaitan ‘yan kasuwa ta hanyar horo da samun rance. Kare haɗarin asarar kuɗi da tabbatar da bin ƙa’idar dokoki da Ƙarfafa amfani da sabbin fasahohin zamani wajen gudanar da harkokin banki.

Ta ƙara da cewa gwamnatin jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda, za ta ci gaba da marawa duk wani shiri baya matuƙar yana da tasiri wajen kawo ci gaba.

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Kwararrun Masanan Harkokin Banki (Chartered Institute of Bankers) reshen jihar Katsina, Malam Sani Magaji, ya yaba ƙwarai da wannan sabuwar hanya da gwamnatin jiha ta bullo da ita.

“Wannan jiha ce ta farko da ta kafa sashen da zai kula da al’amuran da suka shafi hulɗar gwamnati da bankuna. Wannan babban ci gaba ne da ba a taɓa gani ba a sauran jihohin Najeriya,” in ji Ma’aji.

Ya ci gaba da cewa: “Bankuna abokan ci gaba ne. Muna amfani da albarkatunmu wajen tallafa wa kasuwanci da shirye-shiryen gwamnati. Muna jin daɗi da wannan damar da aka ba mu domin mu bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.”

Ya kuma yi alƙawarin cewa bankunan kasuwanci a jihar Katsina za su kasance cikin shiri wajen bayar da gudunmawar da ake buƙata da kuma ayyukan al’umma, domin ci gaban jihar gaba ɗaya.

Taron ya ƙare da sahalewar dukkanin masu ruwa da tsaki cewa za a ci gaba da haɗin kai domin gina kyakkyawan tsarin hada-hadar kudi da zai amfani jama’ar jihar Katsina.

Follow Us