SHUGABA TINUBU YA ZIYARCI KANO DOMIN YIN TA’AZIYYAR MARIGAYI AMINU DANTATA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes18072025_195359_FB_IMG_1752868384734.jpg


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano, inda ya bayyana marigayi Alhaji Aminu Dantata a matsayin gwarzo, mutumin kirki, jajirtacce, mai sadaukar da kansa wajen jin ƙai da tallafa wa al’umma. Shugaban ya ce rayuwar Alhaji Dantata cike take da yawan ibada, hidima, da ɗabi’un kirki waɗanda suka kasance abin koyi ga kowa.

Marigayi Dantata ya rasu ne a Dubai ranar Asabar, 28 ga Yuni, 2025 yana da shekaru 94, kuma an yi jana’izarsa a Madina a ranar Talata 1 ga Yuli. Shugaba Tinubu ya bayyana ziyarar a matsayin ta musamman, yana mai cewa Dantata ba wai babban mutum ne kawai a kasuwanci ba, ɗan gida ne a wurinsa. Ya kuma tuna yadda ya nemi addu’o’insa kafin zaɓen 2023.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna godiya ga Shugaban Ƙasa bisa jajantawa da goyon bayan da ya bai wa iyalan marigayin da kuma al’ummar jihar. Ya ce bayan rasuwar Dantata, Shugaban Ƙasa ya tura tawagar gwamnatin tarayya zuwa Saudiyya karkashin jagorancin Ministan Tsaro, sannan ya sake turo Mataimakin Shugaban Ƙasa da wasu ministoci domin ta’aziyya, kafin daga bisani ya je da kansa duk da tarin aikinsa.

A jawabinsa, ɗan marigayin, Alhaji Tajudeen Aminu Dantata, ya nuna matuƙar godiya ga Shugaban Ƙasa bisa wannan karamci da karramawa da ya nuna. Ya tabbatar da cewa za su ci gaba da riƙe ƙimomin da mahaifinsu ya bari. Taron ta’aziyyar ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Mataimakinsa Sanata Barau Jibrin, Gwamnan Jigawa, da attajirai irin su Alhaji Aliko Dangote da Alhaji Mohammed Indimi.

Follow Us