...Me ya faru? Ya aka yi?
Daga Binciken musamman na jaridun Katsina Times
Yayin da Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua da ke jihar Katsina ke cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi na matsalar kuɗi, wanda kodayashe suna wajen gwamnatin jihar Katsina da ƙoƙon bara da buƙatu daban-daban waɗanda suke neman a warware masu don ba su da kuɗin aiwatar da su.
A daidai lokacin da gwamnatoci ke ƙarfafa wa manyan makarantun gwiwa su nemo hanyar samun kuɗin shiga.
Jaridun Katsina sun gano wasu mutane ma'aikatan Jami'ar su 26 da ake bin bashin zunzurutun kuɗi har Naira milyan 512,995,572,63.
A jadawalin sunayen da jaridun Katsina Times suka samu daga sashen kuɗi na Jami'ar ya nuna waɗansu malaman ana bin su bashin kuɗin sama da shekaru biyar, amma ba su biya ba har ya zuwa lokacin da muke rubuta wannan rahoton.
YA SUKA CI BASHIN JAMI'AR?
Kowace Jami'a tana da tsarin inganta ayyukanta ta hanyar tura malamanta karatu don su ƙaro ilmi su dawo Jami'ar su koyar a bisa tsarin da za su mayar da kuɗin da aka kashe masu wajen ƙaro ilmi.
Jami'ar Umaru Musa 'Yar'adua da kyakkyawar manufa ta riƙa tura waɗannan malaman zuwa ƙasashen wajen domin su samo ilmin su dawo gida su ingnata harkar ilmin Jami'ar.
Abin takaici sai sun samo ilmin sun dawo, ba za su biya Jami'a kuɗin da ta kashe masu ba, ba kuma za su yi mata aikin da za su mayar da kuɗin da aka kashe masu ba, sai kawai su samu wani aikin da ya fi na Jami'ar sai su gudu su koma can.
Daga jadawalin sunayen da jaridun Katsina Times suka samu sun ga har da wani wanda ba ɗan jihar Katsina ba, an kwashi kuɗin Jami'ar sama da Naira milyan 34 aka ba shi horo, kuma ya gudu ya bar Jami'ar.
Wani abin takaici da jaridun Katsina Times ta gano mafi yawan waɗanda suka nuna ba za su biya kuɗin ba sun ci banza, suna da halin biyan kuɗin a inda suke aiki, ko kuma muƙamin da suke riƙe da shi.
Jaridun Katsina Times sun bi diddigin duk sunayen da ake bi bashin da inda suke aiki a yanzu. Cikin mutane 26, 18 kuɗaɗen da Jami'ar ke bin su ba wani kuɗi ba ne a wajensu a inda suke aiki.
Misali wani da aka kashe wa miliyan 88 da kuma wani da aka kashe wa milyan 45, inda sun sun so suna iya nunka kuɗin biyar su ba Jami'ar, kuma a jikinsu.
Bincikenmu ya gano Hukumar Jami'ar ta ɗau shekaru tana bin hanyoyin lalama, amma lamarin kullum sai ƙara muni yake yi.
Bincikenmu ya gano cewa wasu ke hana waɗansu biya, suna faɗa masu cewa kar su biya ba abun da zai faru.
Akwai zargin da jaridun Katsina Times suka kasa tabbatarwa na cewa waɗanda ake bi bashi suna magana a tsakaninsu a kan cewa su ƙi biya kawai.
Wannan zargin ba mu tabbatar da shi ba, amma aikin waɗansu da ake bi bashin na nuna kamar haka.
Akwai zargin cewa wani Farfesa da ya shugabanci kwamitin amso bashin ya riƙa jan ƙafa da sanya aikin ya riƙa tafiyar hawainiya.
MATSAYAR JAMI'AR A KAN LAMARIN
Dakta Ali Muktar, ɗaya daga cikin mataimakan shugaban Jami'ar ya tabbatar wa da jaridun Katsina Times cewa, wasu sun rubuta alƙawarin za su riƙa biya a hankali daga lokacin da suka samu sabon aiki.
Ya ce, wasu kuma tafiyarsu suka yi ba tare da faɗa wa Jami'ar ba, duk kuwa da sun san cewa akwai bashi Jami'ar a kansu.
Dakta Ali Muktar ya ƙara da cewa, "Ganin cewa duk waɗanda ake bi bashin 'yan Katsina ne -in ban da ɗaya ko biyu-, shi ya sa muka yi ta bin lamarin da lalama."
Ya ƙara da cewa, "Amma a zaman Hukumar Gudanarwa na Jami'ar ta yi ranar 25 ga Afrilu, 2025, ta ba Hukumar makarantar damar ta ɗau mataki na gaba a kan waɗanda ake bi bashin."
RA'AYIN ƘUNGIYOYI DA MUTANEN GARI
Kwamared Bishir Dauda, sakataren ƙungiyar Muryar Talaka ta ƙasa ya kira abin da malaman Jami'ar da ake bi bashi suka yi a matsayin abin da bai dace ba, ga jihar Katsina da kuma ilmi.
Ya yi kira ga Gwamnan Katsina, Dakta Umar Raɗɗa a matsayinsa na Shugaban Jami'ar ya ɗau tsattsauran mataki a kan waɗannan marasa kishin cigaban ilmi a Katsina.
Dukkanin waɗanda jaridun Katsina Times suka yi magana da su sun yi Allah-wadai da halayyar waɗanda ake bi bashin ba su kuma da niyyar biya.
Wasu kuma sun zargi cewa akwai haɗin baki tsakanin shugabannin Jami'ar da waɗanda ake bi bashi ƙila shi ya sa suka ƙi ɗaukar wani mataki na ƙwato wa da Jami'ar kuɗaɗenta.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
All on All social media platforms