Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya nada Mataimakinsa, Faruq Lawal Jobe, a matsayin Amirul Hajjin Jihar Katsina na shekarar 2025.
Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Abdullahi Garba Faskari ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa tawagar za ta sa ido kan dukkan ayyukan aikin Hajji a gida da Saudiyya, tare da tabbatar da tsaron lafiyar maniyyata.
Mambobin tawagar sun hada da Kakakin Majalisar Jiha, Rt. Hon. Nasiru Yahaya Sai Kwamishinan Harkokin Addinai, Ishaq Shehu Dabai da wasu jamiāan gwamnati da malamai.
Gwamna Radda ya yi fatan Allah ya ba tawagar nasara a aikin Hajji, inda ake sa ran za a fara nan ba da jimawa ba.