SDP Ta Gargadi Masu Kafa Tsarin gudanarwa a cikin jam'iyyar na Bogi a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes16042025_072501_FB_IMG_1744785787257.jpg


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, Talata, 15 Ga Afrilu, 2025:

Shugaban jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) na Jihar Katsina, Alhaji Bello Adamu Safana, ya gargadi wasu mutane da kungiyoyi da ke kafa tsarin gudanarwar jam'iyyar na boge a jihar Katsina ba tare da sahalewa  ba.
Yana mai bayyana hakan a matsayin saba doka.

Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a ofishin jam’iyyar da ke kan titin Kano a birnin Katsina, shugaban jam’iyyar ya jaddada cewa, babu wani mutum ko kungiya da ke da hurumin kafa tsarin gudanarwa da sunan SDP sai idan yana da cikakken rajista kuma an amince da shi daga shugabancin jam’iyyar.

“Muna so mu ja kunnen wasu mutane da kungiyoyi da ke kokarin kafa tsarin gudanarwa na yankuna da sunan SDP. Wannan babban kuskure ne, kuma doka ba ta yarda da hakan ba. Za mu bi doka mu dauki mataki kan duk wanda ya ci gaba da wannan dabi’a,” in ji Safana.

Taron ya samu halartar manyan jami’an jam’iyyar da suka hada da Farfesa Abubakar (Sakataren jam’iyya), Alhaji Mustafa Abdullahi Sani (Shugaban matasa), Alhaji Mustafa Muhammad Kurfi, Alhaji Ali Maiwada Masanawa (Mataimakin Shugaban Sanata a  Katsina), da Dakta Dansarai Ali Magaji (Mataimakin Shugaban Jam’iyya).

A cikin jawabin nasa, shugaban jam’iyyar ya kuma sanar da cewa, a halin yanzu ana ci gaba da raba katin wucin gadi na zama membobin jam’iyyar, sai dai cikin makonni biyu masu zuwa za a fitar da katin zama memba na dindindin.

“Wadannan sabbin katin za su maye gurbin na wucin gadi, kuma za su tabbatar da sake tantance cikakkiyar rajistar membobin jam’iyyar,” in ji shi.

Alhaji Safana ya kara da cewa akwai wasu kungiyoyi masu muhimmanci da ke shirin shiga jam’iyyar SDP a hukumance, kuma tuni jam’iyyar ta shiga tattaunawa da su domin tabbatar da tsari mai kyau da fahimta.

“Kowanne mutum ko kungiya na da damar shiga jam’iyyar SDP, a kowane lokaci. Muna kiran matasa musamman da su zo su shiga wannan jam’iyya mai kishin gaskiya, adalci da kyakkyawan shugabanci,” in ji shugaban.

Ya kammala da tabbatar da cewa jam’iyyar SDP za ta ci gaba da bin gaskiya, adalci da kuma daidaito a dukkan harkokinta, tun daga matakin rajista har zuwa matakin neman takara ko shugabanci.

“Za mu tabbatar da gaskiya da adalci ga kowa, a kowane mataki na jam’iyya. Tsarinmu zai kasance a bude kuma gaskiya ce ginshikinsa,” ya nanata.

An kammala taron da baiwa sauran shugabannin jam’iyyar damar karin bayani ga manema labarai, domin jaddada hadin kai da nagartar tsarin jam’iyyar a Jihar Katsina.

Follow Us