Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar| Katsina Times
An samu ci gaba a shari’ar da ta dabaibaye rikicin da ya faru tsakanin jami’an hukumar Hisbah da fitaccen mawakin jihar Katsina, Alhaji Surajo Mai Asharalle, yayin da wata kotu a jihar ta bayar da belinsa tare da ’ya’yansa biyar, bayan cika wasu sharudda da kotun ta gindaya.
Tun da fari, jami’an hukumar Hisbah sun fuskanci farmaki daga wasu matasa dauke da makamai a unguwar ƙofar Ƙaura yayin gudanar da aikin hana matasa buga kwallo a titi, lamarin da ya jawo tashin hankali da harba bindigar gargajiya da ta jikkata jami’ai shida daga cikin 'yan Hisbah.
A cewar rahoton Hisbah, Alhaji Surajo Mai Asharalle ne ake zargi da harba bindiga lokacin da jami’an suka nemi janye wa bayan fara rikicin. Lamarin ya yi sanadin rauni ga jami’an Hisbah da dama, ciki har da harbin bindiga da jifar duwatsu. Inda aka garzaya da su Babbar Asibitin Katsina, daga bisani aka tura wasu daga cikinsu zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya domin kulawa ta musamman.
Bayan haka, kotu ta bayar da umarnin tsare Alhaji Surajo Mai Asharalle a gidan gyaran hali, inda daga bisani aka dage sauraren karar zuwa ranar Alhamis, 10 ga Afrilu, 2025. Daga baya kuma, kotun ta amince da bayar da belinsa da kuma na ’ya’yansa biyar bisa wasu sharidda da suka cika a ranar Talata 15 ga watan Afrilu.
Amma a ranar 8 ga watan na Afrilu bayan wani zama da neman beli da bai samu ba wasu matasa da 'ya'yan mawakin suka gudanar da zanga-zanga a cikin birnin Katsina domin nuna rashin jin daɗinsu kan tsare shi. Masu zanga-zangar sun rera wakoki da ɗaga alluna suna kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta tabbatar da adalci da bin doka da oda.
A cewar wasu daga cikin shugabannin zanga-zangar, sun bayyana cewa har yanzu ba a yanke hukunci a kotu ba, duk da tsawon lokacin da mawakin ya shafe a tsare, lamarin da suka bayyana a matsayin rashin adalci.
Hukumar Hisbah dai ta bayyana damuwa kan yawaitar hare-hare da ake kai wa jami’anta a jihar, tare da tunatar da wani hari makamancin haka da aka kai watanni biyu da suka gabata.
Yanzu haka, al’ummar jihar Katsina na dakon ganin yadda za a kammala wannan shari’a don tabbatar da adalci a kowane bangarorin biyu.