Kamfanin Wutar Lantarki TCN Ya Karo Sabuwar Transfoma A Abuja

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes14042025_075847_IMG-20250413-WA0099.jpg


A ranar Juma'a ne Kamfanin samar da wutar lantarki a Najeriya ya kawo Sabuwar na’urar taransifoma mai karfin 300MVA a tasharsa ta Katampe da ke Abuja, Sabuwar Transfomar

Kawo wannan Na'ura zai ninka yawan wutar da tashar ta katanfe ke iya samar wa har sau uku, wanda hakan na nufin Babban Birnin Tarayya da makwantan birnin za su kara samin wadatuwar ingantaccen hasken lantarki ga ababen more rayuwa da masana'antu.
Aikin tashar wani ɓangare ne na haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya ta amince da shi tsakanin kamfanin samar da wutar lantarki TCN da Bankin Duniya don haɓaka ƙarfin rarraba wutar a Najeriya.
Ana sa ran wannan ci gaban zai yi tasiri sosai kan yanayin samar da wutar lantarki a Abuja, kuma kokarin da TCN ke yi na inganta hanyoyin sadarwa na kasar na ci gaba da ¹.

Follow Us