ƘUNGIYAR KASUWANCI TA NIJERIYA DA AMURKA TA KARRAMA GWAMNA LAWAL BISA AYYUKAN INGANTA RAYUWAR AL’UMMA A ZAMFARA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes14042025_075544_FB_IMG_1744617232598.jpg



Ƙungiyar Kasuwanci ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal da babbar lambar yabo ta jagoranci da hidimar al’umma.

A ranar Asabar ne ƙungiyar ta yi bikin cika shekaru 65 da kafuwa, tare da ƙaddamar da shugabanta na 20, tare da karrama Amurkawa da 'yan Nijeriya da suka cancanta da kyautuka a otel ɗin Lagos Continental da ke jihar Legas.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, ƙungiyar kasuwanci ta Nijeriya da Amurka ƙungiya ce ta kasuwanci da ke aiki bisa tsarin sai wanda ya kasance mamba, kuma ita ce cibiyar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu ta farko a Nijeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta karrama gwamna Lawal tare da gwamnonin Akwa Ibom, Kaduna, da kuma jihar Legas.

“A jiya a Legas, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da ƙaddamar da Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban ƙungiyar na 20.

“Taron mai taken ‘Ƙarfin Haɗin Kai: Shekaru 65 na inganta dangantakar tattalin arzikin Nijeriya da Amurka’ ya samu halartar manyan jami’an Amurka da Nijeriya da kuma ‘yan kasuwa.

“Ƙungiyar ta amince da goyon bayan da Gwamna Lawal yake baiwa harkokin kasuwanci a jihar Zamfara, musamman a fannin noma.

“Karramawar da aka baiwa gwamnan na nuni ne da irin kwazonsa na jagoranci, da kwazonsa na inganta ilimi, da kuma jajircewarsa wajen magance matsalar rashin tsaro.

“Ƙungiyar ta kuma yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa inganta rayuwar al’ummar Zamfara ta hanyar ba da fifiko wajen samar da kiwon lafiya, ilimi, noma, da kuma ayyukan ƙarfafawa guiwar al'umma.”

Yayin karbar lambar yabon, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirinsa na inganta rayuwar al’ummar Jihar Zamfara ta hanyar inganta ayyukan yi.

"Ina so in gode wa shugabannin ƙungiyar 'yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka da suka ga na cancanci wannan karramawa, hakan zai ƙara min kwarin guiwa na ƙara himma, wannan na ɗaukacin al'ummar jihar Zamfara ne."

Follow Us