Dan Majalisar Tarayya Aminu Balele Ya Jagoranci Taron Addu’ar Ga Mahaifiyar Gwamnan Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11042025_125752_FB_IMG_1744375998968.jpg


Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kurfi da Dutsinma, Alhaji Aminu Balele Dan Arewa, ya jagoranci gagarumin taron addu’ar neman gafara da rahamar Allah ga marigayiya Hajiya Safara’u Umar Bare-Bare, mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina.

An gudanar da taron a babban dakin taro na Jami’ar Tarayya ta Dutsinma (FUDMA), inda ya samu halartar shugabannin kananan hukumomin Kurfi da Dutsinma, da kansilolinsu, da kuma manyan jiga-jigan jam’iyyar APC daga matakin mazaba zuwa karamar hukuma.

Haka zalika, taron ya samu halartar limamai da malamai daga yankunan Kurfi da Dutsinma, tare da wakilan shugabancin jami’ar FUDMA da wasu daga cikin manyan jami’ai na gwamnati da sauran 'yan uwa da abokan arziki.

Bayan kammala addu'o’in, Dan Majalisar ya tallafa wa matasa da kwamfutoci don taimakawa wajen samun sana’a, tare da raba kyautar Naira miliyan goma ga wakilan jam’iyyar da suka halarci taron.

Taron ya gudana cikin kwanciyar hankali, inda aka gudanar da komai lafiya, aka kuma tashi lafiya.

Follow Us