Gwamnatin Jihar Katsina Ta Nada Dr. Musa Ahmed Zayyad a Matsayin Sabon Rector na KSITM

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes10042025_181007_Screenshot_20250410-190830.jpg

Gwamnatin Jihar Katsina, ta hannun Kwamitin Gudanarwa na Katsina State Institute of Technology and Management (KSITM), ta tabbatar da nadin Dr. Musa Ahmed Zayyad, MCPN, MNCS, a matsayin sabon Rector na cibiyar.

Nadin ya bude sabon babi ga ci gaban KSITM, duba da irin gwanintar Dr. Zayyad a fannin ilimi, gudanarwa, da ci gaban fasaha. Ana sa ran cewa jagorancinsa zai kawo sauyi mai ma'ana wajen bunkasa fasahar zamani da horar da matasa a fannonin kimiyya da gudanarwa.

Dr. Zayyad, dan asalin karamar hukumar Katsina, ya mallaki takardun karatu masu daraja daga gida da kasashen waje. Ya kammala digirinsa na Ph.D a fannin Management Information Systems daga Cyprus International University, digiri na biyu (M.Sc) a Information Systems daga Eastern Mediterranean University, da kuma digiri na farko (B.Sc) a Computer Science daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto. Haka kuma, yana da difloma ta digiri na gaba a fannin koyarwa daga Jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta Katsina.

Dr. Zayyad ya yi aiki a matsayin malami da mai gudanarwa a jami’o’i da dama ciki har da Umaru Musa Yar’adua University, Al-Qalam University Katsina, Kampala International University a Uganda, da kuma National Open University of Nigeria (NOUN). Ya taba rike mukamin mai sa ido a waje (external moderator) a KSITM, wanda hakan ya sanya dawowarsa a matsayin Rector na da muhimmanci matuka.

Malami ne da ake girmamawa a fagen ilimi, kuma mamba ne na kwamitin rijistar kwararrun na’urorin kwamfuta na Najeriya (MCPN) da kuma kungiyar kwararrun kwamfuta ta Najeriya (MNCS). Ya jagoranci daliban digiri na gaba, ya halarci tarukan kasa da kasa, ya gudanar da horo ga ma’aikata, kuma ya yi aikin tantancewa a jami’o’i daban-daban.

Dr. Zayyad na da kyakkyawar hangen nesa game da sauyin fasaha, ingancin ilimi da shugabanci mai tasiri, kuma ana sa ran zai gina KSITM a matsayin cibiyar ilimi ta zamani da ke bayar da horo mai amfani ga matasa a Najeriya. Hakan na tafiya da kudurin gwamnatin jihar Katsina na inganta rayuwar matasa ta hanyar samar da ilimi mai nagarta a bangaren fasaha da shugabanci.

Ma’aikata, dalibai da shugabannin KSITM sun taya Dr. Musa Ahmed Zayyad murna bisa wannan mukami, tare da nuna kwarin gwiwa cewa jagorancinsa zai kawo ci gaba mai dorewa da daukaka wa cibiyar.

Follow Us