Sana’ar Hilasko a Katsina: Tarihi, Asali, Amfani da Ƙalubale

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09042025_171423_FB_IMG_1744218644760.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 

Birnin Katsina, daya daga cikin manyan biranen Arewacin Najeriya, ya shahara wajen tarihi, al’adu, sana’o’i da kuma magungunan gargajiya tun asalin kafuwar sa. Daga cikin wadannan magunguna da al’ummar Hausawa suka girmama saboda amfani da su wajen gyara lafiya, musamman wanke ciki da dawo da karfi, akwai wani magani da aka fi sani da Hilasko — magani mai dogon tarihi wanda ya samo asali tun cikin daruruwan shekarun da suka gabata.

Hilasko wani ganye ne mai asali da ya samu karbuwa a cikin kabilar Hausa-fulani har ake ganin sa a matsayin maganin gargajiya na hausawa, da aka yi imani yana taimakawa wajen wanke ciki, kawar da majina, da kuma dawo da kuzari. Litattafan musulunci sun ambaci amfaninsa, lamarin da ya kara masa kima wajen Hausawa da ma sauran mabiya addinin Musulunci, a fadin Duniya 

A wani binciken da Katsina Times ta gudanar, an gano cewa sana’ar saida Hilasko a Katsina ta samo asali ne daga tsohuwar unguwar Masanawa, inda wata tsohuwa mai suna Hajiya Mai Sa’ida ta shahara wajen hada da saida maganin fiye da shekaru dari da goma sha biyar da suka wuce.

A tattaunawa da muka yi da daya daga cikin jikokinta, Yusuf Ibrahim wanda aka fi sani da Yusuf Soja, ya bayyana cewa:

 “Kakarmu Hajiya Mai Sa’ida ta fara sana’ar Hilasko a kusan shekarar 1916, kuma ta gada ne daga kakanninta mata na kabilar Bugaje (Buzaye). Sana’ar tana gudana a matsayin gadon gado a cikin dangi, daga ita zuwa babban danta Alhaji Ibrahim Mai Hilasko, daga bisani zuwa babban dansa Alhaji Salisu wanda ya dawo daga Jamhuriyar Nijar bayan yakin basasa a shekarar 1970. Daga karshe ni kuma na karba, yanzu shekaru 39 kenan ina gudanar da sana’ar.” ya bayyana.

Yusuf Soja ya bayyana cewa ana hada Hilasko ne da sinadarai guda goma sha daya, inda ya ce:

 “Akwai nau’o’in ganyen Hilasko guda biyar, amma mu muna amfani da nau’in da ake kira "Dan Asbinawa (Azbin). Daga cikin kayan hadin akwai kanwa da kimba, amma saboda sauyin zamani da yawaitar cututtuka kamar ulcer da hawan jini, na rage amfani da su domin kare lafiyar masu amfani.” Inji shi.

Yusuf Soja ya jaddada cewa sana’ar Hilasko ta zama abar dogaro ga rayuwarsa da iyalinsa, kuma yana da dimbin mabukata daga ciki da wajen jihar Katsina:

 “Tun lokacin da na fara, ban taba fuskantar korafi ko matsala daga wanda ya sha Hilasko ba. Maganin ya zamo abin dogaro ga mutane da dama, musamman a lokacin watan azumi da kafin shigarsa. Duk da haka, amfani da Hilasko ba sai ana azumi ba, domin yana da kyau a sha shi a kalla sau daya a kowane wata domin tsaftace ciki.”

Ya kuma kara da cewa: “Yanzu akwai gidajen hada Hilasko fiye da goma a cikin Katsina, amma alhamdulillah na samu daukaka saboda sadaukarwa da ingancin sana’a. A lokacin azumi, mutane suna fitowa daga ko’ina don sayen Hilasko.” a wajena.

Duk da nasarorin da sana’ar ke samu, masana sun bayyana cewa akwai bukatar a samar da tsarin rijista da kulawa daga hukumomin lafiya domin kare lafiyar masu amfani da kuma tabbatar da ingancin kayayyakin gargajiya. Haka kuma, akwai bukatar fadakar da jama’a game da yadda za su iya amfani dashi busa ka'ida da ta dace da jiki da lafiya.

Hilasko ya wuce magani kawai – ya zama al’ada, tarihi da wata hanya ta tabbatar da cigaban masana'antar gargajiya a Arewacin Najeriya. Duk da cewa duniya na cigaba da rungumar magungunan zamani, irin wannan tarihi na Yusuf Soja na bayyana cewa akwai bukatar Karfafa gwiwa wajen inganta magungunan gargajiya, kare su da kuma jirkita su da tsarin kimiyya domin jin dadin al’umma.

Za ku iya kallon cikakkiyar tattaunawar mu da Yusuf Soja a shafukanmu na Katsina City News da Katsina Times a dukkan kafafen sada zumunta.

Follow Us