Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
A wani mataki na ƙarfafa karatu da fasahar zamani a jihar Katsina, an kaddamar da shirin “Window on America” a sashen ɗakin karatu na ƙasa reshen jihar Katsina, haɗin gwiwar da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya. Wannan shirin zai zama cibiyar yada ilimi, fasaha da ƙarfafa hulɗar al’adu tsakanin Najeriya da Amurka, musamman ga matasa da dalibai.
A yayin bikin kaddamarwar da aka gudanar a ranar Talata, 9 ga Afrilu, 2025, Babban Mai Shari’a na Jihar Katsina, Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar, ya yaba da wannan yunkuri tare da bukatar hukumomi da cibiyoyi da su tabbatar da amfani da cibiyar ta hanyar shiryawa da aiwatar da shirye-shiryen ilimi da nishaɗi ga al’umma.
A cewarsa: “Zamu tabbatar da cewa gwamnati na da hannu a wannan aiki. Katsina jihar tarihi ce da ilimi. Amma abin takaici ne yadda wasu matasa ‘yan jami’a ke shiga harkar laifi ta yanar gizo. Saboda haka, dole ne mu kare wannan wuri daga wannan dabi'a marar kyau.”
Ya ƙara da cewa zai tuntuɓi Gwamnan jihar don bada gudunmawa da halartar wasu daga cikin shirye-shiryen cibiyar, yana mai jaddada muhimmancin fasahar zamani da rawar da take takawa wajen ci gaban jama’a.
Shugabar sashen ɗakin karatu ta ƙasa reshen jihar Katsina, Hajiya Amina Maje Sayyadi, ta bayyana cewa cibiyar zata bayar da dama ga matasa wajen samun horo kan ilimi, shirye-shiryen sauyin yanayi, rubuce-rubuce da kuma jagoranci. Ta ce: “Muna da shirye-shirye da dama da za mu iya aiwatarwa tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki. Akwai horo kan yadda ake neman guraben karatu a jami’o’in Amurka, shirye-shiryen rubuce-rubuce, da kuma tattaunawa da jakadu daga Amurka.”
Ta nuna farin cikinta da yadda cibiyar ta Katsina ta samu amincewa daga ofishin jakadancin Amurka, duk da cewa ba su zo jihar da kansu ba, sai hotuna kawai aka tura musu kuma suka amince da fara aikin. “Daga cikin rassan ɗakin karatu na ƙasa guda 33, Katsina ce kaɗai suka zaba,” inji ta.
A nasa jawabin, Daraktan shirin Window on America na Katsina, ya yaba da haɗin gwiwar da ake da ita tsakanin cibiyar da sauran hukumomi. Ya ce: “Mun saba da yin tarukanmu a nan ɗakin karatu, kuma muna fatan ci gaba da shiryawa a nan a kowane mako, domin ganin cewa cibiyar na aiki yadda ya kamata.”
Bikin kaddamarwar ya samu halartar manyan baƙi daga hukumomin ilimi da na gwamnati, ciki har da jami’ai daga Kwalejin Gudanar da Harkokin Mulki ta jihar Katsina, da Hukumar Gudanarwar Makarantun Sakandire, da kuma kungiyoyin Dalibai.
A ƙarshe, an yaba da wannan ƙoƙari na gwamnatin Amurka da hadin gwiwar Najeriya wajen kafa cibiyar, wanda zai taimaka wajen farfaɗo da Ilimi ,al’adu da samar da damammakin koyo da haɓaka karatu a tsakanin matasa da ɗalibai a jihar Katsina.