Tawagar Sasanci Ta Ƙungiyar ECOWAS Ta Sake Zuwa Jamhuriyar Nijar...

top-news

Tsohon Shugaban Najeriya Abdulsalam Abubakar da Sarkin Musulmi sun sake komawa jamhuriyar Nijar karo na biyu domin sasanci tsakanin Sojojin ƙasar da kuma ƙungiyar.

Prime Minister na Niger, Lamine Zeine shine ya tarbe su tare da zantawa dasu, tawagar taje da niyyar ganawa da Abdulrahman Tchiani amma dai an tunanin cewa wani yunƙuri dake faruwa a fadar shugaban ƙasar ta Nijar ya hana ganawar.

Ana dai tunanin kamar wasu Sojojin dake gadin fadar shugaban ƙasar suna bore yanayin da yasa aka samu rashin tabbas.

A wuri ɗaya kuma ƙungiyoyin mata ne suke zanga zangar lumana a babban birnin Niamey inda suke nuna goyon bayan su ga Sojojin ƙasar tare da neman Buƙatar Sojojin Faransa da su fice subar ƙasar ta Nijar baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *