Tarihin Sana'ar Alkubus a Katsina: Hajiya Assibi Ta Bayyana Yadda Ta Shafe Shekaru 70 Cikin Nasara

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes29032025_233210_FB_IMG_1743291031519.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

A cikin tarihin kasuwanci da sana'o'i a jihar Katsina, akwai wasu da suka shafe tsawon rayuwarsu suna gudanar da sana'o'in da suka zame musu garkuwa, daya daga cikinsu ita ce Hajiya Safiya, da aka fi sani da Hajiya Assibi mai Alkubus ko "Assibi Kwaya". Tana da shekaru 94 a duniya kuma ta shafe sama da shekaru 70 tana sana'ar dafa da saida Alkubus da miya a garin Katsina. A wata tattaunawa da ta yi da jaridar Katsina Times, ta bayyana irin nasarorin da ta samu da kuma sirrin da ya sa kasuwancinta ya dore har tsawon wannan lokaci.

Hajiya Assibi ta bayyana cewa ta fara sana'ar Alkubus tun tana da shekaru 15, a zamanin Sarkin Katsina Usman Nagogo. A lokacin, tana saida Alkubus da sukari a faranti. Da ikon Allah, kasuwancinta ya bunkasa cikin kankanin lokaci, inda kwastomominta suka bata  shawarar da ta rika yi da miya. Tace tana tuna yadda ta shawarci mijinta kan hakan, wanda ya yi mata kashedi akan yiwuwar asara idan ba a sayar ba. Sai ta ce, "Idan ba a sayar ba, zan ci sauran, idan ma ya wuce haka, zan ba da sadaka." Wannan kyakkyawar niyya ta taimaka wajen nasarar sana'arta.

Hajiya Assibi ta jaddada cewa sirrin nasararta a sana'a shi ne tsafta, amana da ingancin abinci. Ta tabbatar da cewa tana dafa abinci mai kyau wanda ke burge kwastomominta. "Ba zan taba sayar da wani abinci ba in ba shi da kyau. Ina tabbatar da tsafta da inganci," in ji ta. Wannan dabi'a ta sa Alkubus dinta ya yi suna, har mutane daga wasu jihohi da kasashen ketare ke zuwa don siyan abincinta.

A tsawon shekaru da ta shafe tana kasuwanci, Hajiya Assibi ta samu albarkar zuwa Makka don sauke farali sau da dama. Ba ita kadai ba, har da 'Ya'ya da jikokin ta ta kaisu Makka don sauke farali. Duk da wannan nasara, ta bayyana cewa ba ta taba zuwa aikin Umra ba.

Suna da mutuntakar da Hajiya Assibi ta samu ba kawai ga kwastomominta bane, har ma da manyan mutane. Ta yi hulda da gwamnoni, ministoci da shugabannin kasa daban-daban a cikin kasar nan. Abincinta ya shahara sosai ta kasance fitacciya a fannin Sana'ar Alkubus a jihar Katsina.

Duk da cewa shekaru sun ja kuma ba ta iya gudanar da sana'ar kamar da, jikokinta sun dauki sana'ar da muhimmanci, suna ci gaba da tafiyar da ita kamar yadda ta koyar. Har yanzu, sunanta yana nan daram a zukatan mutanen Katsina, domin kowa ya san ta ko da kuwa bai taba cin abincinta ba.

A karshe, Hajiya Assibi ta bayyana cewa tana cikin koshin lafiya, ba ta da wata damuwa sai yawan shekaru. "Alhamdulillah, ina jin dadi, kuma babu wata matsala sai dai shekaru sun ja," in ji ta.

Muna fatan ci gaba da jin irin gudunmawar da Hajiya Assibi ta bayar a rayuwa, da kuma ganin matasa sun dauki darasi daga irin jajircewarta a fagen kasuwanci. Za ku iya kallon cikakken tattaunawarta a shafukanmu na Katsina City News a Facebook da sauran kafafen sada zumunta.

Follow Us